Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-25 15:13:56    
An kammala ayyukan ranar farko wajen mika wutar yola ta gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing a Girka

cri
An kunna wutar yola ta gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing ta shekarar 2008 jiya 24 ga wata a Olympia ta kasar Girka. Daga bisani ne, aka fara gudanar da aikin mika wutar yola. Da maraicen jiya ne, aka kai wutar yolar birnin Mesologi, mai tazarar kilomita 130 daga arewa maso yammacin Olympia. Hakan ya kawo karshen ayyukan ranar farko wajen mika wutar yola.

Da karfe 8 da rabi na dare, agogon wurin, a lambun shan iska mai suna Hero dake cibiyar birnin Mesologi, kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics na kasar Girka ya hada kansa tare da hukumar wurin domin shirya wani kasaitaccen bikin maraba da zuwan wutar yola ta gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing.

An ce, za a shafe kwanaki 7 ana ratsa birane 43 domin mika wutar yola a yankin Girka, kuma tsawon hanyar da za a bi ya kai kilomita 1528, masu mika wutar yola sama da 600 ne za su shiga aikin mika wutar yolar. A lokacin, za a shirya bikin maraba da wutar yola a birni na karshe da za a kai ma wutar yola a kowace rana.(Murtala)