Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-25 09:34:09    
Masu karanta shafin yanar gizo na Jamus sun nuna bakin cikinsu ga rahoton da gidan talibijin na RTL ya bayar kan hargitsin Lhasa

cri
A kwanan baya, masu karanta shafin yanar gizo na Jamus sun nuna bakin cikinsu ga rahotannin da gidan talibijin na RTL na kasar ya bayar kan hargitsin nuna karfin tuwo da aka yi a birnin Lhasa na jihar Tibet ta kasar Sin.

Wani mai karanta shafin yanar gizo da ya sa suna "Franz" ya ce, rahotannin da ba na gaskiya ba da wasu kafofin yada labaru na kasar Jamus, ciki har da gidan talibijin na RTL suka bayar abin kunya ne ga dukkan kafofin yada labaru na kasar Jamus. Wasu kafofin yada labaru na kasar Jamus suna nuna bambanci ga kasar Sin. Suna son yin amfani da rahotannin da suka bayar domin yunkurin kin halartar gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing da kebe yankin Tibet daga kasar Sin.

Wasu masu karanta shafin yanar gizo sun kuma rubuta cewa, mutanen kasar Jamus da yawa ba su san kasar Sin ba, suna fahimtar kasar Sin ne daga bayanai da labaru da ba na gaskiya ba da wasu kafofin yada labaru suka bayar bayan da suka zaba ko suka murkushe. Wani mai karanta shafin yanar gizo na Jamus ya kuma rubuta cewa, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, wasu kafofin yada labaru na Jamus su kan kai suka ga kasar Sin, domin kasar Sin tana ta samun cigaba a cikin 'yan shekarun nan, amma wasu kasashen yammacin duniya ba su samu cigaba ba. Wani mai karanta shafin yanar gizo wanda ke yin aikin ba da jagorancin yawon shakatawa ya ce, ya kamata wasu mutanen kasar Jamus wadanda suke nuna bambanci ga kasar Sin su fahimta, mene ne zai faru idan kowace kabilar kasar Sin wadda take da kabilu 56 ta nemi kafa wata kasa da kanta. (Sanusi Chen)