Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-25 08:56:16    
Jami'in kwamitin shirya gasar Olympics na Beijing ya yaba wa bikin daukar wutar wasannin Olympics a kasar Girka

cri

A ran 24 ga wata an dauki wuta mai tsabta a birnin Olympia na kasar Girka domin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing ta shekarar 2008. Sabo da haka, jami'in kwamitin shirya gasar ya yaba wa bikin daukar wutar wasannin Olympics da aka shirya da kokarin da bangarorin kasar Girka suka yi.

Mr. Liu Jingmin, mataimakin magajin birnin Beijing, kuma mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing ya ce, "bangaren kasar Girka ya yi dimbin ayyuka. Yau shugaba da firayin minista na kasar Girka da magajin birnin Olympia da ministoci da yawa na gwamnatin kasar Girka sun halarci bikin daukar wuta mai tsaba, wannan yana alamanta zumuncin da ke kasancewa a tsakanin jama'ar Girka da ta kasar Sin."

Mr. Jiang Xiaoyu, mataimakin shugaban zartaswa daban na kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing yana tsammani cewa an ci nasarar daukar wuta mai tsaba. Ya ce, "an shirya wani gagarumin bikin daukar wuta mai tsaba da ke cike da al'adun Olympic. Ba ma kawai wannan biki yana nuna tsabta na ruhun Olympic da ba a iya kai masa farmaki ba, kuma yana bayyana cewa, tabbatar da zaman lafiya buri daya ne na jama'ar duk duniya. Muna fatan za a kara yada wannan ruhun neman zaman lafiya da abuta da cigaba a duk duniya. Ana kuma bayyana ruhun neman jituwa a gun wannan biki." (Sanusi Chen)