Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-25 11:17:06    
Yunkurin rukunin Dalai Lama na sanya batun Tibet a karkashin kulawar kasa da kasa zai ci tura

cri
A kwanan baya, Lhakpa Phuntsok, babban darektan cibiyar nazarin ilmin Tibet ta kasar Sin ya bayyana cewa, yunkurin rukunin Dalai Lama na sanya batun Tibet a karkashin kulawar kasa da kasa zai ci tura.

Lhakpa Phuntsok, wanda ya taba zama mataimakin shugaban jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, ya yi bayani da cewa, rukunin Dalai Lama ya yi yunkurin sanya batun Tibet a karkashin kulawar kasa da kasa, ya kuma yi abubuwa da yawa domin cimma burinsa. A can da har zuwa yanzu, wasu bangarori na kai ruwa rana na kasashen duniya suna mara wa rukunin Dalai Lama baya wajen gudanar da aikace-aikacen kawo wa kasar Sin baraka, sun kuma yi amfani da wadannan aikace-aikacen. In babu wadanda ke mara masa baya, to, rukunin Dalai Lama ba zai kasance ba.

Lhakpa Phuntsok yana ganin cewa, Dalai Lama na 14 ya daga tutar addini, yana kawo wa kasar Sin baraka da yin zangon kasa ga hadin kan al'ummomi bisa hujjar addini, shi ya sa a maimakon mai bin addini na gaskiya, shi wani dan siyasa ne da ke gudun hijira, yana kuma kawo wa kasar Sin baraka.

Ya kuma yi nazarin cewa, ko da masu neman 'yancin kan Tibet na gida da na waje suna hada kansu, amma ba su iya canza tarihi da batun gaskiya ba, wato jihar Tibet, wani bangare ne na kasar Sin. A can da, ba su iya samun 'yancin kan Tibet ba, yanzu ba za su iya ba, nan gaba kuwa, ba za su iya ba.(Tasallah)