Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 21:51:38    
Wadanda suka sa wuta kan kantuna biyu a birnin Lhasa sun amsa laifinsu

cri
A gun taron manema labarai da aka yi yau a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar tsaron jama'a ta kasar Sin, Madam Shan Huimin ta fayyace cewa, yanzu an kama mutane biyar da suka sa wuta ga kantuna biyu, wato wani kantin sayar da tufafi a birnin Lhasa da kuma wani kantin sai da babura a gundumar Dazi, a tarzomar da aka samu a ranar 14 ga watan nan da muke ciki, wadanda har suka haddasa mutuwar mutane da dama, kuma masu laifin sun amsa laifinsu.

Madam Shan Huimin ta ce, yanzu kurar tarzomar ta lafa, kuma an maido da oda a birnin Lhasa. Jama'a 'yan kabilu daban daban a jihar Tibet suna nuna tsayayyen goyon baya ga matakai daban daban da gwamnati ta dauka da kuma yadda hukumomin tsaron jama'a suka hukunta masu laifi. A lokacin da 'yan sanda da sojoji suke kulawa da al'amarin, sun yi matukar hakuri, kuma ko kadan ba su yi amfani da miyagun makamai ba. A yayin da suke kulawa da al'amarin kuma, gaba daya akwai 'yan sanda da sojoji 242 da suka ji raunuka.(Lubabatu)