A 'yan kwanakin baya, kasashen duniya sun ci gaba da nuna fahimta da goyon baya ga jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin da ta daidaita matsalar tashe tashen hankali da suka hada da fasa kayayyaki, da kwashe kayayyakin jama'a, da cunnama wurare wuta a birnin Lhasa.
Gwamnatin kasar Cuba ta bayar da wata sanarwa, inda ta bayyana cewa, 'yan a-ware sun aikata ayyukan nuna karfin tuwo a jihar Tibet, wannan ya haddasa mutuwar jama'a da kuma jin raunukansu da babbar hasarar dukiyoyinsu, da nufin lalata gasar wasannin Olympics ta Beijing, sabo da haka ne, gwamnatin kasar Cuba ta yi suka kan haka da babbar murya. Rushe ofishoshin jakadancin kasar Sin a ketare ya saba wa yarjejeniyar diplomasiya ta Vienna. Gwamnatin kasar Cuba tana tsayawa kan adawa da ko wane irin kulle kullen tsoma baki cikin harkokin gida na Sin, da lalata mulkin kasar Sin da kuma cikakken yankinta.
Ban da wannan kuma, kasashen Venezuela, da Turkmenistan, da Comoros, da Iraki, da Oman, da Mongolia su ma sun ci gaba da nuna fahimta da goyon baya ga jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ta daidaita wannan matsalar tashe tashen hankali da suka hada da fasa kayayyaki, da kwashe kayayyakin jama'a, da cunnama wurare wuta a birnin Lhasa.(Danladi)
|