Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 21:33:48    
An mayar da al'amura kamar yadda suka yi a da a birnin Lhasa,babban birnin jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta

cri

A tsakiyar watan Maris na wannan shekarar da muke ciki,tsirarru masu bin addinin Bhutan na birnin Lhasa hedikwatar jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta suka ta da tarzoma bisa makarkashiya da tarkacen Dalai lama suka kulla kuma suna ta zugarsu,har sun shuka barna ga zaman lafiya da kwanciyar hankali na birnin Lhasa.Bayan da al'amarin ya faru, gwamnatin jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta dauki matakai kan wadanda suka aikata miyagun laifuka bisa dokoki.yanzu kurar tarzoma ta lafa a birnin, shaguna da makarantu da kusuwanni suke tafiyar da harkokinsu yadda suka yi a da.

A ran 23 ga wata,wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya ganama idonsa yadda shaguna sama da metan sun bude kofofinsu suna tafiyar da harkokinsu yadda ya kamata a unguwar kasuwanci ta birnin Lhasa.ban da wannan kuma ana iya ganin mazaunan birnin da baki maso yawon shakatawa na kasashen waje suna yawo a lanbunan shan iska da babban filin birnin.Mr Guzman da ya zo daga kasar Italiya ya ce a ran 14 ga watan Maris ya ga tarzoma da ta faru a titunan birnin Lhasa,yana jin tsoron a lokacin.kwanan baya kome na tafiya yadda ya kamata a birnin Lhasa,yana jin dadin zama a birnin ya ce,

Ina cikin shirin ganawa da wasu aminaina,yau da safe na je kasuwa in saye ganyayen ci, na kuma cin abinci a wani dakin sayar da abinci da tsakar rana,zan tafi waje domin yin yawon shan iska.

Mr Yang Fees Derek wanda ya zo birnin Lhasa daga kasar Swiden yau da wata daya da wani keken hawa Masaukin da ya ke zama a ciki a hanyar matasa,wuri ne da aka samu tarzoma mai tsanani.Mr Derek ya gaya wa wakilinmu cewa a ran 14 ga watan Maris da yamma ya ji wasu mutane suna kuwwa a waje da dakinsa,hayaki na tashi a wurare da dama,ya fice a guje zuwa kan titi, ya ganema idanunsa yadda masu ta da tarzoma sun yi dauki ba dadi da wasoso da kone kone. A cikin kwanaki biyu na baya,kura ta lafa,Mr Derek ya wannan birnin yana da kyaun gani sosai.

Aran 15 da ran 16 ga watan Maris, 'yan sanda suna tafiyar da ayyukansu na kiyaye zama da oda a kan tituna. Ban kara ganin tashin hankula ba kurar ta lafa.Idan ka je kasuwa kamar babu wani al'amarin da ya faru ba,al'amuran sun koma yadda suka yi a da.

Kwanann baya wasu kasuwannin sayar da kayayyakin aikin gona da kasuwanni sun tafiyar da harkokinsu.A kasuwa mai suna Baiyi,wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya yi hira da buduwa mai suna Xiong.

"Ina aiki a wurin nan na kusa,na kan sayi abubuwa daga wannan kasuwa. Mutanen sun yi yawa cikin kwanaki biyu na baya kamar a da,kayayyaki barkatai sun cika kasuwa,farashin abubuwa bai haura ba,babu sauyin da aka samu."

A cikin tarzoma da aka faru a birnin Lhasa, yan bata gari sun kai hare hare kan makarntu da dama. Masu ta da tarzoma sun kai hari kan ginin koyarwa na makarantar firamare na Haichen dake cikin birnin Lhasa a ran 14 ga watan Maris. Domin kare lafiyar 'yan makarantaar,makarantar firamare ta Haichen ta dakatar da koyarwa har kwanaki uku. Ga shi a yau makarantar Haichen ta koma yadda ta kasance a da,yaran suna yin wasa a filin makaranta.shugaban makarantar Mr Nyima Tsering ya ce,

"kashi 98 cikin kashi dari na daukacin 'yan makaranta sun koma,dukkan malaman koyarwa ma sun koma kan guraban ayyukansu."

A cikin tarzoma da ta barke a rn 14 ga watan Maris,layin wayar samar da wutar lantarki mai tsawon kilomita 12.5 dake cikin birnin ya sha lahani mai tsanani,haka kuma babban ofishin kula da wutar lantarki ya sha lahani.Tarzoma ta haddasa mugun tasiri ga mutane masu amfani da wayoyi na gida da na wayoyin salula,an kuma kone wasu layin gidan talabiji.sassan da abin ya shafa sun kokarta wajen gyara su. A halin yanzu an mayar da wutar lantarki ga yawancin mazaunan birnin Lhasa da kantuna yadda ya kamata.wayoyin sadarwa da na talabiji sun fara aiki yadda ya kamata. A kan muhimman titunan birnin Lhasa,wakilin gidan rediyon yaga motocin taxi da motocin bus bus da motoci masu dogon zango suna tafiya daidai.A gaban fadar Budala masu bin addi sun yi yawa.Magajin garin birnin Lhasa Dorje Tserup ya bayyana cewa,

"Mun tsaya tsayin daka mu yi bincike da dauki ga wadanda suka aikata miyagun laifuffuka wajen ta da tarzoma,ba mu nuna tausayi ga mai laifi ba.muna cike da imani wajen kiyaye zaman kwanciyar hankali da oda a birnin Lhasa yadda ya kamata."(Ali)