Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 20:09:42    
An fara mika wutar yola na wasannin Olympics na Beijing a kasar Girika

cri

Bayan da aka kunna wutar yola ta wasannin Olympics na birnin Beijing a yau 24 ga wata a birnin Olympia, nan da nan ne aka fara mika wutar wadda za a shafe tsawon mako guda ana bikin mika ta a yankin Girika. An ce, a rana ta farko, za a tashi daga tsohon gari na Olympia, wato inda aka sami asalin wasannin Olympics, sa'an nan, za a bi ta birnin Patras a mika wutar har zuwa birnin Messologi da ke yammacin kasar Girika.

An ce, za a ratsa yankuna 16 da birane 43 na kasar Girika wajen mika wutar, kuma tsawon hanyar da za a bi zai kai kilomita 1528. Bayan haka, mutane 605 za su shiga aikin nan na mika wutar yola a yankin Girika.(Lubabatu)