A ran 23 ga wata, tashar internet ta gidan Telebijin na RTL na kasar Jamus ta bayar da wata sanarwa a shafin internet, inda ta amince da bayar da labarai marasa gaskiya game da lamarin nuna karfin tuwo a jihar Tibet ta kasar Sin.
A 'yan kwanakin baya, tashar internet ta gidan telebijin na RTL ta bayar da wani hoto, inda 'yan sanda 4 suka kori masu zanga zanga da sandarsu, kuma aka bayyana cewa, ' 'yan sanda na kasar Sin suka murkushe masu zanga zanga a Tibet.' A ran 23 ga wata, wannan tashar internet ta amince da kuskurenta, a hakika dai, abin da wannan hoto ya nuna shi ne, 'yan sanda na kasar Nepal suna korar masu zanga zanga a birnin Kathmandu, babban birnin kasar. Sabo da haka ne, wannan tashar internet ta amince da kuskurenta, kuma ta nuna bakin ciki game da haka.(Danladi)
|