Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 15:29:32    
Yin wasannin Olympic zai kara wa kasashen duniya fahimtar kasar Sin wadda a bude take, in ji Mr. Rogge

cri

Shugaban kwamitin wasannin Olympic na duniya wato IOC Jacques Rogge ya furta a ran 23 ga wata a birnin Olympia na kasar Greece cewa, wasannin Olympic na Beijing zai kara wa kasashen duniya fahimtar kasar Sin wadda a bude take, ta yadda zai kawo wa kasar Sin kyawawan sauye-sauye.

Mr. Rogge zai halarci bikin kunna wutar yula ta wasannin Olympic na Beijing a ran 24 ga wata a birnin Olympia. Ya jaddada a cikin wata sanarwa cewa, yin wasannin Olympic a kasar Sin zai sa mutanen duniya kashi 1 cikin 5 su iya shiga cikin wasannin Olympic kai tsaye, zai yada tunanin Olympic sosai. Ya kara da cewa, nauyin da aka dora wa kwamitin Olympic na duniya shi ne, samar wa 'yan wasan kasashen duniya wani dandalin yin gasa cikin adalci, shi ba wata kungiyar siyasa ko wata hukuma mai tsatsauren ra'ayi ba ne.

Mr. Rogge ya kuma nuna cewa, kwamitin wasannin Olympic na duniya zai cigaba da hada gwiwa sosai tare da kwamitin kula da wasannin Olympic na Beijing don tabbatar da yin wasannin Olympic na Beijing cikin nasara.(Lami)