Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 15:20:21    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- A yayin da ranar bikin hawa kan kolin tudun Everest wato Jumo langma don mika wa juna wutar yola ta wasannin Olimpic ke kusantowa, sassa da yawa ciki har da yawon shakatawa da yanayin sama da sufuri na jihar Tibet suna nan suna kokarin share fage daga fannoni daban-daban domin mika wa juna wutar yola da yin yawon shakatawa dangane da wasannin Olimpic.

Mr. Yu Yungui, sakataren J.K.S. ta hukumar yawon shakatawa ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, jihar Tibet ta kaddamar da kayayyakin yawon shakatawa na wasannin Olimpic da ake kira "Hau kan kolin tudun Jumo langma don mika wa juna wutar yola ta wasannin Olimpic, da yin yawon shakatawa a ganiyar duniya dangane da wasannin Olimpic", kuma za su yi hidima ga masu yawon shakatawa na kasar Sin da na kasashen waje domin hawa kan kolin tudun Jumo langma.

Bisa bayanin da hukumar yawon shakatawa ta jihar Tibet ta bayar an ce, a lokacin da za a mika wa juna wutar yola ta wasannin Olimpic, hukumar za ta bude hanyoyi 3 da za a bi domin yawon shakatawa ta hanyar hau kan kolin tudun Jumo langma.

Kolin tudun Jumo langma shi ne koli mafi tsayi na duniya, wato tsayinsa ya kai mita 8,844.43 daga leburin teku.

---- Kwanan baya mun sami labari daga wajen hukumar al'adu ta lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin cewa, za a bude bikin baje-kolin kasar Sin na shekarar 2008 kan kayayyakin fasaha na jama'a 'yan kabilun kasashen duniya da na hajjojin yawon shakatawa da na al'adu daga ran 16 zuwa ran 20 ga watan Yuli na wannan shekara a cibiyar nune-nunen kayayyakin kasahen duniya da ke birnin Kunming na kasar Sin.

An ce, karo na farko ne za a shirya wannan bikin baje-koli, kayayyakin da za a nuna a gun bikin sun kasu kashi 11 ciki har da sassakakkun kayayyaki, da tufafi, da kayan kida, da kayayyakin yawon shakatawa, da duwatsu masu ban ta'ajibi kuma masu daraja, fadin nunin kuma ya kai murabba'in mita 10,000.

A lokacin kuwa, da akwai kwararru 'yan fasaha tsakanin jama'a 'yan kabilu da masana'antu na wurare daban-daban na duk kasar Sin za su shiga bikin baje-koli, ban da wannan kuma 'yan kasuwa masu fitar da kayayyakin fasaha da masu sayar da kayayyakin na kasashen Japan da Korea ta kudu da shiyyoyin Asiya ta gabas da Asiya ta kudu maso gabas da Turai da kuma nahiyar Amurka za su zo birnin Kunming na nan kasar Sin don hallartar bikin.(Umaru)