Mr Lutz Kraft, mai shekaru kimanin 50 da haihuwa a bana dan kasar Jamus ne. Yau da shekaru 12 da suka wuce, wato a farkon shekarar 1995, kamfanin Siemens ya yanke shawarar kafa wani reshensa na yin kayayyakin wutar lantarki a kasar Sin. Sa'an nan ya turo Mr Lutz Kraft zuwa kasar, don zaben wurin da zai kafa wannan reshe. A farkon yanayin bazara na waccan shekara, Mr Luts Kraft dauke da dalar Amurka miliyan 9 da abokan aikinsa da dama sun sauka birnin Hangzhou, wanda ake nuna masa yabo cewa, ya yi kamar aljannar duniya. Da saukarsu a birnin ke da wuya, sai suka nuna kauna ga birnin, sa'an nan Mr Lutz Kraft ya gabatar da shawara a kan kafa reshen kamfanin yin kayayyakin wutar lantarki na Siemens a birnin Hangzhou, daga bisani kuma kamfanin ya amince da shawararsu.
Abubuwan da suka faru sun tabbatar da cewa, Mr Lutz Kraft ya nuna hangen nesa wajen gabatar da shawara don bunkasa harkokin kamfanin Siemens a birnin Hangzhou. A cikin 'yan shekaru da suka gabata, reshen kamfanin yin kayayyakin wutar lantarki na Siemens ya sami bunkasuwa cikin sauri sosai har fiye da yadda ake tsamani. Da Mr Lutz Kraft ya tabo magana a kan kamfaninsa, sai ya bayyana cewa, "wani abun da na iya tabbatarwa, shi ne kasuwannin kasar Sin suna ci sosai. Ana bukatar kayayyakinmu masu dimbin yawa a kasar Sin. Dalilan da suka sa kamfaninmu ya iya samun bunkasuwa cikin sauri sosai, su ne domin muka hada gargajiyar kasar Sin da fasahar kasar Jamus da kyau, kuma birnin Hangzhou ya fi dacewa da mu idan an kwatanta shi da sauran wurare na kasar Sin."
Amma a ganin ma'aikatan kamfaninsa, mai gidansu Lutz Kraft ma wani babban dalilin ne da ya sa kamfanin ya iya samun sakamako mai kyau sosai. Mr Xuan Gelun, tsohon ma'aikacin kamfanin yin kayayyakin wutar lantarki na Siemens da ke a birnin Hangzhou ya bayyana cewa, yana jin farin ciki da aikinsa, sabo da mai gidansa Lutz Kraft ya ba shi isasshiyar damar nuna kwarewarsa. Ya kara da cewa, "Mr Lutz Kraft mai gidanmu yana nuna hangen nesa sosai. Kamfaninmu ya sami babban ci gaba a cikin shekaru sama da 10 da suka wuce. Idan mai gidanmu bai iya nuna hangen nesa ba, to, tabbas ne, kamfaninmu ba zai iya samun ci gaba kamar haka ba. Yanzu ma kamfaninmu ya kan sami bunkasuwa cikin sauri a ko wace shekara. "
Madam Chen Ming wadda ke kula da aikin jigilar kayayyaki a kamfanin ita ma ta amince da ra'ayin abokin aikinta sosai cewa, wani babban dalilin daban da ya sa Mr Lutz Kraft ya iya jagorancin kamfaninsa da ya samun kyakkyawan sakamako kamar haka shi ne, domin idon basarar da yake nuna a kasuwa. Ta kara da cewa, "a ganina, bisa matsayinsa na wani babban jami'in kamfaninmu, Mr Lutz Kraft yana nuna hangen nesa. Ya nuna idon basira sosai a kasuwa, kuma ya nuna hangen nesa ga makomar bunkasuwar kamfanin, ya yi aikinsa da kyau sosai. Ina ganin cewa, yana taka rawa sosai wajen kula da kamfaninmu."
A shekarar 2001, Mr Lutz Kraft ya sami "lambar girma ta amincin duniya" da hukumar kula da gwanayen kasashen ketare ta kasar Sin ta ba shi. Bayan shekaru uku kuma, hukumar birnin Hangzhou ta ba shi kyakkyawan lakabi kamar haka "dan birni mai girmamawa na Hangzhou. A shekarar bara, Mr Kutz Kraft wanda ya shafe shekaru 10 yana zama a birnin Hangzhou ya sami izinin zaman dukkan rayuwarsa a kasar Sin. (Halilu)
|