Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 14:50:30    
Jaridar "Toronto Star" ta bayar da dogon cikakken bayani kan lamarin da mutanen Tibet suka yi

cri

Jaridar "Toronto Star" ta bayar da dogon cikakken bayani kan lamarin da mutanen Tibet suka yi na nuna karfin tuwo wanda masu yawon shakatawa na kasar Canada suka gani da idannunsu. Bayanin ya bayyana cewa, Kenwude mai shekaru 19 da haihuwa da ya zo daga birnin Victoria shi da idannunsa na kansa ya ga yadda mutanen Tibet suka kai wa mutanen kabilar Han hari da yi musu duke-duke, ciki har da wani saurayin da ke hawan babur ya mutu bisa duke-duken da aka yi masa sosai.

Mr Alex Sinclaire mai shekaru 40 da haihuwa da ya zo daga birnin Wingewa ya bayyana cewa, a ranar da aka haddasa lamarin nuna karfin tuwo, ya boye a wurin da ke da matakin hawan ginin gidan waya, ya ji karar bindiga da karar fashewar bom. Ya ce, lokacin shi ne lokacin da ya ji bakin ciki sosai, a gaskiya dai, lokacin shi ne lokacin da na ji damuwa a raina sosai.

Amma, Madam Susan Wetmore mai shekaru 59 da haihuwa wadda ta zo ne daga birnin London na lardin Ontario ba ta yi shirin bayyana lokaci maras kyau sosai da ta shige ba, ta ce, ba zan iya bayyana abubuwan da na ji na gani ba, har zuwa yanzu dai ina neman tsirar da kaina daga halin da na taba shiga ciki. Ta bayyana cewa, wasu abubuwa mummuna ne sosai, kai, mummuna sosai da sosai.

Mr Kenwude mai yawon shakatawa na kasar Canada da muka taba taba gabatar da shi a baya , kafin ya tashi daga birnin Lhasa, ya karbi ziyarar waya da wakilin jaridar "Torondo Star" ya yi masa, ya bayyana cewa, bayan da ya sami iznin tashi daga Hotel, ya ga shara a ko'ina a kan babbar hanyar titin Beijing na birnin Lhasa tare da wasu motocin da aka riga aka kone su.

Mr Kenwude ya bayyana cewa, wurin ya riga ya zama birnin dodo, an kone shaguna da kantuna da yawa. Na tabbatar da cewa, mutane da yawa sun mutu bisa sakamakon tashin gobara.

Mr Kenwude ya kuma waiwayi lamarin cewa, a ranar da aka haddasa lamarin, yana dab da wurin da ke dab da dakin Ibada na Dazhaosi. Yana ganin cewa, a lokacin da Motocin daukar fashinjoji da babura suke zirga-zirga suke wucewa, sai mutanen Tibet suka tare su, duk wadanda suke da alamar kalmomin harshen Han, wato Sinanci, sai aka kone su ko aka kwace baburansu ko lalata su sosai. Wani abu maras kyau sosai da ya faru a gaban Mr Kenwude shi ne , wasu mutanen Tibet sun tare wani saurayin kabilar Han da ke kan babur ta hanyar jefa masa dutse, amma saurayin bai san wane abu ne ya faru ba, ya sanya wani hulan kwano mai launin zinariya a kansa, ya bar babur, ya daga hannayensa a sama, bai san yadda zai yi ba. Amma, sa'annan kuma, wasu 'yan fashi yawansu kusan 15 da ke rike da sandunan karfe a hannunsu, sun soma dukan saurayin, bayan da wadannan 'yan fashi suka kayar da shi, sai suka ci gaba da dukansa, dadin dadawa kuma sun cire masa hulan kwano don ci gaba da dukan kansa.

Mr Kenwude ya gaya wa wakilin jaridar "Toronto Star" cewa, a ganisa , yana iya tabbatarr da cewa, saurayin ya mutu, jininsa ya bazu a ko'ina har a kan fuskarsa, ba a iya banbanta cewar wai shi wane ne ba.

Alex Sinclaire da ke zama kasar Britaniya yanzu shi ne malamin da ke aiki a wata jami'a, ya ce, duk abubuwan da ya ji ya gani a birnin Lhasa, ga alama tamkar bangarorin biyu sun riga suka yi shiri ne sosai domin lamarin nan. Kafin yini daya da faruwar lamarin, wato ranar 13 ga watan Maris, sun je yawon shakatawa a dakin ibada na Sanye, amma a rabin hanyar da suka bi, wasu 'yan sanda sun shiga motar da suke ciki don duddubawa.

'Yan sandan ba su duba Passport ba, amma sun roki mabiya addinin Buddah da mata masu bin addinin Buddah da su sauka daga motar da muke ciki, amma ba masu yawon shakatawa na kasashen waje ba. Yanzu, da muke waiwayon abubuwan nan, sai muka fahimci cewa, hukumar kasar Sin ta riga ta sani cewa, za a haddasa hargitsi a wurin.

A karshe dai dogon bayani na jaridar "Toronto Star" ya bayyana cewa, kodayake wadannan masu yawon shakatawa na kasar Canada sun ji tsoro da wahaloli daga lamarin nan da an iya fahimtar da cewa, amma dukkansu sun yi magana a kan wani abu cewa, a lokacin da suke jihar Tibet da sauran wuraren kasar Sin, ko hukumar kasar Sin ko mutanen Tibet dukkansu sun yi musu maraba sosai da sosai.

Madam Wetmore ta bayyana cewa, kodayake mun ga wasu abubuwa masu ban tsoro da kuma masu tausayi sosai, kuma mun ga wasu abubuwa masu ban mamaki, amma an yi mana kulawa sosai da sosai.(Halima)