Jama'a masu sauraro asalam laikum,barkanku da war haka,barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan lokaci. A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayanin musamman da wakilan gidan rediyo na kasar Sin suka shirya kan labaran da kafofin yada labarai na kasashen waje suka bayar kan bakin da ke yawon shakatawa a jihar Tibet yayin da tarzoma ta tashi a birnin Lhasa.
Jairdar "Times" ta kasar Britaniya ta buga wani bayani a ran 19 ga watan Maris wanda ya ke da lakabi haka "masu yawon shakatawa sun girgiza da nuna fargaba kan tarzoma da ta tashi a jihar Tibet" inda ta bayyana abin da masu yawon shakatawa da suka bar Tibet ba dadewa ba suka ganamma idanunsu yayin da tarzoma tabarke.
Jaridar Times ta ce yayin da baki masu yawo shakatawa da suka bar Tibet suka bayyana yadda tarzoma ta gudana cikin kwanaki biyu a makon da ya shige, dukkansu sun girgiza da fargaba, musamman yayin da suka ga mutanen Tibet masu ta da tarzoma suke dukan mutanen Han matafiya a kan hanya da kanana duwatsu.
Baki masu yawon shakatawa na kasashen yamma da suka ga abun da ya faru sun bayyana cewa gungunn masu ta da tarzoma sun zura idanunsu kan mutanen da suke da kamannin mutanen kabilar Han da kayayyakinsu,sun yidauki ba dadi ga masu basukur da buge su da sandunan karfe,sannan sun kone motocinsu.
Jaridar Tmes ta yi sharhi cewa bayanan da masu yawon shakatawa na kasashen yamma suka yi sun tabbatar da cewa 'yan tarzoma sun nuna rashin imani,ba ma kawai sun yi wa zaman lafiya da wadatuwar jihar Tibet zagon kasa ba har ma sun karya shawarar rashin amfani da karfin tuwo da Dalailama ya tsaya a kai.
"kan abin da ya wakana a Lhasa da wuya a zabi wani gefe a tsaya tare da shi",wannan bayani da wani dalibi mai suna Keywood na kasar Canada mai yawan shekaru 19 da haihuwa ya gaya wa 'yan jarida yayin da ya isa birnin Kathmandu,babban birni na kasar Nepal a ran 18 ga watarn Maris.Keywood da ya yi yawon shakatawa na kwanaki goma a birin Lhasa ya yi nuni da cewa,"ina amincewa da ra'ayin mutanen Tibet su mallaki al'adunsu amma ba na goyon bayan kome daga cikin abubuwan suka aikata."
Keywood ya tunasar da cewa yayin da yake tafiya a hanyar Beijing dake cikin birnin Lhasa, ya ga motocin soja guda hudu da suka tsaya a kan hanyar Ramoche Temple,sa a wannan lokaci wasu 'yan tarzoma sun jefa wa motoci manyan duwatsu, sun farfasa glass na motocin. Kimanin 'yan sanda masu damara talatin ko arba'in dauke da garkuwa sun sauka daga motocin. 'yan sandan sun toshe hanyoyin,nan take mutanen Tibet masu ta da tarzoma sun yi wa 'yan sandan zobe,sun fara jifarsi da duwatsu.Keywood ya ce ya ganam idonsa motoci guda uku dauke da akwatunan duwatsu,amma bai san wane ne ya samar da wadannan duwatsu ga wadannan 'yan tarzoma ba.
Bayan mintuna kalilan Keywood ya ga matasa biyu ko ukuna 'yan tarzoma na Tibet suna gudu a kan hanyar Ramoche Temple yayin da 'yansan sun isa wurin,a wannan sa'I wani gungun'yan tarzoma suna tafe da matasan,ba tare da bata lokaci mai tsawo ba sun dawo sun fara dauki ba dadi kan shagunan mutanen kabilar Han da matafiya.
Keywood ya gaya wa jaridar Times cewa ya ganamma idonsa 'yan tarzoma na Tibet sun kai bugu kan mutanen Han a kalla biyar, ciki har da wani a kan basukur da aka kada shi a gefen hanya. Keywood ya ce a karshen makon jiya yana wani hotel a karshen hanyar Beijin ta gabas, yana iya jin karar bindigogi da karar harsasai masu sa hawaye,shi bai ga wata motar soja da wuce a wajen ba.
Yayin da ya tashi daga birnin Lhasa,Keywood ya ce yawancin makarantu da shaguna da hukumomi sun fara tafiyar da harkokinsu yadda ya kamata, mutanen Tibet da na Ghan sun fara zirga zirgaa titunan birnin. Keywood ya ce yayin da mahukuntan birnin suka bukaci masuta da tarzoma da su mika kansu kafin wa'adin karshe, ba a ga matasa 'yan Tibet da yawa a titunan birnin Lhasa ba.
Mr Claude Ba;soger,dan yawon shakatawa na kasar Switzerland wanda ya ke da shekaru 25 da haihuwa ya isa birnin Lhasa a ran 8 ga watan maris,shi ma ya bayyana abinda ya gani bayan da ya isa Kathmandu daga Tibet,musamman ya ga yadda wani tsoho a kan keke da ya sha duka mai tsanani a hannun'yan tarzoma. Ya ce masu ta da tarzoma sun yi kuwwa kamar kuraye a haukace, sun yi dauki ba dadi kan duk kayayyaki da mutane da suke da nasaba da mutanen kabilar Han.
Mr Balsiger ya bayyana wa jaridar Times yadda ya ga wani dan bude ido na kasa Canada ya shiga kasada wajen ceton wani mutum na kabilar Han.Ya ce halin da ake ciki a Lhasa ya yi tsanani,bisa maganar da mutnen wurin suka yi,an ce mutane sama da dari sun rasa rayukansu,an kuma kama mutanen sama da dubu.Balsiger ya bar birnin Lhasa a ran 17 ga watan Maris ya yi dare a hotel na dab da filin jiragen sama,ran 18 ga watan Maris ya sauka birnin Kathmandu ta jirgin sama.
Mr Stephen Thompson mai shekaru 41 da haihuwa ya zo ne daga kasar New Zealand,yayin da tarzoma ta wakana a birnin Lhasa,ya sauka a hotel din Saikang ba da dadewa ba.Ya ga yadda masu ta da tarzoma suka farfasa gilas na gine gine. Mr Thompson ya ce. ba mu jin tsoro ba,wasu 'yan tawagar masu yawon shakatawa sun yi fargaba,wani bako mai yawon bude ido ya ji rauni saboda duwatsun da aka jefa masa,wasu kuma sun ji rauni a ka."(Ali)
|