Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 11:56:11    
Kullum kasar Sin tana girmama 'yancin jama'a

cri
Ran 23 ga wata, Qin Gang, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya amsa tambayoyin da manema labaru suka yi masa game da wai majalisar harkokin waje ta kasar Amurka ta ce, watakila za a sa ido kan 'yan kallo na Amurka da za su kalli gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Wani manemin labaru ya yi tambayar cewa, a ran 20 ga wata, hukumar harkokin kananan jakadu na majalisar harkokin waje ta kasar Amurka ta gabatar da littafin ba da jagoranci ga kallon gasar wasannin Olympic ta Beijing, inda ta ce, mai yiwuwa ne za a kula da harkokin tsaron zaman lafiya a cikin dukkan otel-otel da gine-ginen ofisoshi a Beijing, shi ya sa da kyar za a tabbatar da 'yancin 'yan kallo na Amurka. Mane ne ra'ayin kasar Sin?

Kakakin Sin ya yi bayani da cewa, kasar Sin ba za ta tsara ajandar musamman ba, za ta kuma dauki matakan tabbatar da tsaron zaman lafiya kamar yadda kasashen duniya suke dauka a cikin wuraren al'umma da otel-otel da gine-ginen ofisoshin da dai makamantansu a kasar Sin. Kasar Sin tana kiyaye 'yancin jama'a bisa doka, shi ya sa masu yawon shakatawa na ketare ba su bukatar nuna damuwa. Hukumar harkokin kananan jakadu na majalisar harkokin waje ta Amurka ba ta sauke nauyi bisa wuyanta ba ta yi irin wannan bayani a cikin littafin ba da jagorancin.(Tasallah)