A kwanakin baya, an sami al'amarin ta da manyan laifuffuka masu tsanani sosai a cikin birnin Lhasa na jihar Tibet, jama'ar kasar Sin suna lura da wannan sosai, bi da bi ne suka nuna goyon baya ga matakan da gwamnati ta dauka domin hana ayyukan ta da laifuffuka, da mayar da tsarin zaman al'umma, kuma sun bukaci a hukunta masu yin laifuffuka bisa doka.
Mr. Ngapoi Ganqen Puntsok na kabilar Tibet wanda ke aiki a Beijing ya ce, yawancin mutanen kabilar Tibet suna son zaman kwanciyar hankali, ko shakka ba bu masu tada manyan laifuffuka ba su iya wakiltar mutane masu yawa na kabilar Tibet ba. Mr. Fan Jingjing wanda ke aiki a banki ya yi fushi sosai ga mugun aikace-aikacen da masu ta da hankali suka yi, ya ce, matakan da gwamnati ta dauka sun yi daidai, saboda kiyaye zaman karko shi ne wani aiki na gwamnati.
|