Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 10:42:41    
An fallasa wasu kafofin watsa labaru na kasashen duniya sun watsa labaru masu jabu kan batun jihar Tibet

cri

Ran 20 ga wata, wata mashahuriyar tashar Internet na Sinanci, wato www.duoweinews.com ta bayar da wani labari da wani mutum mai suna Yue Dongxiao ya rubuta, inda ya fallasa wasu kafofin watsa labaru na kasashen duniya da suka watsa labarun jabu kan batun jihar Tibet. A cikin wannan labari, ya ce,

Bayan tashin hankali ya faru a jihar Tibet, mai yiyuwa ne saboda 'yan sanda ba su da mutane sosai, ba su je wurin cikin lokaci domin kama mutane masu yin manyan laifuffuka ba. Idan mun kalli Video da aka dauka, za mu iya ganin 'yan ta'adda masu yawa suna tada hankali ko ina. Don haka za mu yi wata tabaya, ina 'yan sanda suke, ina doka?

Amma, kafofin watsa labaru masu yawa na kasashen Turai kamar CNN, sun watsa Video cewa wai sojojin kasar Sin suna kwantar da 'yan neman 'yancin kan Tibet. Tashar Internet ta CNN ta bayar da wani hoto, a cikin wannan hoto, akwai wata motar soja, wani mutum yana gaban motar, ya yi kamar wannan motar soja za ta murkushe wannan mutum. Amma a gaskiya an yanki rabin wannan hoto ne na bangaren dama, inda mutane masu tada hankali ke yin hare-hare ga wannan mota.

Wasu jaridun kasar Jamus sun bayar da wani hoto, inda 'yan sanda suke bugun mutane masu yin zanga-zanga tare da bayanin cewa, kasar Sin tana kwatar da Tibet. Amma idan mun kalli da hankali za mu iya gane ashe 'yan sanda na kasar Nepal ne.

A kan Internet akwai wani Video, inda mutane masu tada hankali suke bugun wani mutumin da bai ji ba bai gani ba a kansa. Dukkansu suna cikin tashar Internet na www.youtube.com, idan ka nemi "Tibet" a kan tashar Youtube, za mu iya ganin wani Video mai suna "Tibet was is and always will be a part of China" har sau fiye da miliyan daya.

Abin gaskiya shi ne, har ma Dalai Lama ya kalli Video na tashin hankali da kansa, ya ce zai yi murabus daga mukaminsa domin ja layi tsakaninsa da mutane masu tada hankali.