Kasar Sin ta nuna fim din da ke bayyana me ya faru a tashin hankali na Lhasa [Akwai Video]
cri
Ran 20 ga wata, gidan telibijin na kasar Sin wato CCTV ya nuna fim din da ke bayyana lamarin tashin hankali da ya faru a ran 14 ga watan Maris a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, inda aka yi karin bayani game da wannan lamari. A cikin fim din, ana iya ganin cewa, masu tarzoma sun kai hare-hare ga masu wucewa da fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba, haka kuma, sun kona shaguna da gine-gine da yawa da ke gefunan hanya.
Ran 14 ga wata da safe, daga gidan ibada na Ramoche da ke arewa maso gabashin Lhasa, wasu masu bin addinin Buddha sun jefa duwatsu ga 'yan sanda da ke yin aikin sintiri a titi, daga baya, wasu masu tarzoma sun fara taruwa a tituna, sun yi ihu, sun kira take domin kawo wa kasar Sin baraka, sun kuma yi duke-duke, da fasa kayayyaki, da kwace kayayyaki, da cunnama abubuwa wuta, a cikin gajeren lokaci lamarin ya bazu a birnin.
A cibiyar Lhasa, masu tarzomar sun kona shaguna da kantuna da dakunan cin abinci daya bayan daya. A wani shagon sayar da tufafi da aka kone, ma'aikata 5 'yan mata sun mutu saboda sun gaza tsira. Drolma, ma'aikaciyar wannan shago ce kacal da ta tsira daga gobara. Ta gaya mana me ya faru a lokacin. Ta ce,'Sun fasa kofar shagonmu ta gilas duka. Mun ji tsoro kwarai, mun yi kuka, ko wanenmu jikinmu na rawa, ba mu ce kome ba. A can da ban yi zaton hakan ba. A ran nan da safe mun yi aiki tare, amma ba zato ba tsammani lamarin ya faru. Ina son in tambayi wadannan masu tarzomar, donme kuka kashe mutane masu yawan haka da ba su ji ba, ba su gani ba? '
A cikin tashin hankalin da aka yi a Lhasa, masu tarzoma sun yi aikace-aikacen rashin tausayi ainun. Har ma sun kai hare-hare ga likitocin da suke yi wa masu jin rauni jiyya. Losel Tsering, wani likita da ke aiki a asibitin jama'a ta Lhasa ya ji rauni saboda an duka shi, ya gaya mana cewa,'Mun gamu da masu tarzomar a titi, mun nuna musu cewa, mu ne likitoci, amma ba su ji ba, sun fasa motarmu, sun kuma duka mu.'
A Lhasa, masu tarzomar sun kai munanan hare-hare ga gine-ginen samar da wutar lantarki da aikin sadarwa da bankuna da asibitoci da kuma makarantun midil da na firamare.
Bayan aukuwar tashin hankali a Lhasa, hukumar jihar Tibet ta aika da 'yan sanda domin kiyaye odar zaman al'ummar kasa da kiyaye lafiyar mutane da dukiyoyinsu. Bisa hotunan da aka nuna a telibijin, 'yan sanda ba su yi amfani da makamai ba a lokacin da suke gudanar da aiki, sun rike da garkuwa a hannu domin kare kansu da kuma wargaza masu tarzomar, amma masu tarzomar sun kai musu hare-hare da duwatsu da biriki da wuka.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a cikin tashin hankali da aka yi a Lhasa, masu tarzomar sun kona gidaje da shaguna 216, sun fasa da kuma kone motoci 56, sun kuma kone ko kuma kashe wadanda ba su ji ba, ba su gani ba 13. Padma Tsinle, wani jami'in hukumar jihar Tibet ya bayyana cewa, akwai isassun abubuwan shaida da suka nuna cewa, tashin hankali da ya faru a Lhasa, harkar shuka barna ce da rukunin Dalai Lama ya shirya a asiri. Ya ce,'Rukunin Dalai Lama ya tuntubi wasu masu bin addinin Buddha a jihar Tibet ta hanyoyi daban daban, ya kuma ba da umurni ga Tibet ta hanyoyi daban daban. Sa'an nan kuma, ta hanyoyi daban daban ne rukunin Dalai Lama ya zuga da kuma cutar fararen hula da ba su san abun gaskiya ba da su shiga wannan tashin hankalin da tsirarrun mutane suka haddasa.'
Hukumomin jihar Tibet da abin ya shafa sun yi karin bayanin cewa, ya zuwa ran 19 ga wata misalin karfe 10 da dare, mutane kusan 170 da suke da hannu a cikin tashe-tashen hankula na Lhasa sun ba da kansu. Ran 20 ga wata, a muhimman yankuna da tituna na birnin Lhasa, motoci na kaiwa da kawowa cikin 'yancin kai, yawancin shanguna sun maido da ayyukansu, jami'o'i da makarantun midil da firamare sun koma karatu, a galibi dai an maido da odar zaman al'ummar kasa a jihar Tibet.(Tasallah)