Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-21 18:28:38    
Ana tabbatar da hasashen ' taron wasannin Olympic cikin kyakkyawan yanayi a cibiyar wasan tseren kwale-kwale ta birnin Qingdao na kasar Sin

cri

Aminai 'yan Afrika, a matsayin daya daga cikin birane guda shida dake bada taimako ga taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, birnin Qingdao zai dauki nauyin gudanar da gasar tseren kwale-kwale ta taron wasannin Olympic na Beijing. An soma gina cibiyar wasan tseren kwale-kwale ta Qingdao ne a ran 25 ga watan Mayu na shekarar 2004. Kawo yanzu dai, an rigaya an kammala gina ginshikin ginin, wanda kuma za a kammala gina shi duka-duka a karshen shekarar da muke ciki. Ana kokarin tabbatar da hasashen ' wasannin Olympic cikin kyakkyawan yanayi' tun da aka yi fasalin ginin da kuma soma gina shi.

Cibiyar wasan tseren kwale-kwale ta birnin Qingdao tana bakin kogin Fushan dake sabuwar unguwa a gabashin birnin Qingdao, fadin cibiyar ya kai kimanin kadada 45. Ban da wurin gasar tseren kwale-kwale na taron wasannin Olympics, sauran gine-ginen da suka danganta da ginin cibiyar su ma suna cikin cibiyar birnin, wadanda suka hada da kauyen wasannin Olympic, da cibiyar 'yan wasa, da cibiyar kula da harkokin hukumomi, da cibiyar kafofin yada labarai da kuma cibiyar samar da guzuri da dai sauran gine-gine.

Mr. Li Zhipeng, ministan ayyuka da kiyaye muhalli na kwamitin shirya gasar tseren kwale-kwale na Qingdao ya fada wa wakilinmu, cewa a duk tsawon lokacin da ake gina cibiyar wasan kwale-kwale ta Qingdao, ana yin amfani da fasahohin zamani na kiyaye muhalli na gida da waje domin aiwatar da hasashen kiyaye muhalli na taron wasannin Olympic na Beijing. Ya furta cewa: " Taron wasannin Olympic na Beijing ya kaddamar a hasashe iri uku wato ' Taron wasannin Olympic cikin kyakkyawan yanayi, da taron wasannin Olympic na kimiyya da fasaha da kuma taron wasannin Olympic na zamantakewar al'adu. Gwamnatin birnin Qingdao ita ma tana sa ran tabbatar da aikin kiyaye muhalli ta fuskar kimiyya da fasaha na zamani domin gudanar da wata gagarumar gasar tseren kwale-kwale dake da sigar musamman".

Kazalika, Mr. Li Zhipeng ya bayyana cewa, ana matukar kokari wajen yin amfani da kimiyya da kyawawan fasahohi a fannin kiyaye muhalli domin samar da kyakkyawan yanayi a lokacin da ake gina cibiyar wasan kwale-kwale na Olympic. Wadannan fasahohi sun hada da fasahar samun makamashi daga hasken rana, da fasahar yin amfani da na'ura mai aiki da karfin ruwan teku wajen samar da makamashi da kuma fasahar samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da karfin iska da dai sauransu. Mr. Li Zhipeng ya kara da cewa: " Yin amfani da wadannan nau'rori masu kiyaye muhalli zai kara fadakar da jama'a wajen fahimtar hasashen ' Taron wasannin Olympics cikin kyakkyawan yanayi'. Mun lashi takobin yin amfani da wadannan fasahohi na zamani a cikin cibiyarmu ta wasan kwale-kwale. Hakan zai bada misalin koyo sosai a duk zamantakewar al'ummar kasar".

Jama'a masu sauraro, aikin samar da ingantaccen abinci, wani muhimmin aiki ne daban dake gaban cibiyar din. Madam Shan Liang ta bayyna wa wakilinmu cewa : "Gwamnatin birnin Qingdao ta kafa wata cibiyar musamman ta samar da ingantaccen abinci. A lokaci daya, muna bukatar 'yan kasuwa masu bada hidimomi da su tafiyar da harkokinsu daidai bisa ma'aunan da abin ya shafa da ake aiwatarwa tsakanin kasa da kasa".

Yanzu, lokaci ya yi kasa da shekara guda da ta rage a gudanar da taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008. Muka cike da imanin cewa, gasar wasan kwale-kwale da za a gudunar a Qingdao za ta kasance wata kasaitacciyar gasa mai matsayin koli wadda kuma take da sigar musamman. ( Sani Wang)