Yau dai, za mu kawo muku wani bayani kan cibiyar wasannin motsa jiki ta Qinhuangdao. Tuni a watan Yuli na shekarar 2004 ne aka kammala gina wannan cibiya da kuma soma amfani da ita a hukumance, wadda kuma ta kasance wani babban filin wasan motsa jiki na farko da aka somagina shi da yin afmani da shi bayan da aka kammala gina shi dake cikin rassan filayen wasa na gasannin kwallon kafa na taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.
Cibiyar wasannin motsa jiki ta Qinhuangdao tana a bakin teku a unguwar Haigang ta birnin Qinhuangdao. Fadin ginin cibiyar ta kai murabba'in-mita 74,600; kuma jimlar kudin da aka kashe wajen gina ta ta kai kudin Sin wato RMB Yuan miliyan 150. Wannan cibiyar wasannin motsa jiki na iya daukar 'yan kallo kimanin 30,000. Abu mai sha'awa shi ne, idan an duba ginin cibiyar mai hawa shida daga can nesa, to za a iya ganin cewa siffar ginin tana kama da wani kwale-kwale dake tafiya kan teku.
Ya kasance da kyakkyawan tsarin tsaro na zamani a wannan cibiya, inda ke da kyamarorin telebijin 185. Ban da wannan kuma, an kafa wani rumbun tattara bayanai a cikin wannan cibiya, wanda yake hada da tsarin sayar da tikitoci da na dudduba tikitocin, wato ke nan daga cibiyar sarrafe-sarrafe ne ake iya duba yadda 'yan kallo suke shiga cikin filin wasannin ba tare da bata lokaci ba. Hakan zai iya hana wasu mutane shiga cikin filin wasannin dauke da tikitocin jabu. Domin jarraba harkokin duk filin wasannin da kuma bada tabbaci ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing lami-lafiya, gwamnatin birnin Qinhuangdao ta dauki bakuncin shirya wasu jerin gasanni na cikin kasar da wajenta bayan da aka kammala gina filin wasannin.
Mr. Zhao Qinghua, mataimakin babban manajan kamfanin bunkasa wasannin motsa jiki na birnin Qinhuangdao ya furta cewa: " Bayan da aka kammala gina wannan filin wasanni, mun dauki bakuncin gudanar da wassu gaggaruman gasanni daya bayan daya, misali kamar taron wasannin motsa jiki na lardin Liaoning, da gasar kwallon kafa tsakanin wasu mutane taurari da kuma gasannin ja-in-ja a fannin wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar kasar Sin da ta kasar Japan, da tsakanin kungiyar kasar Sin da ta kasar Thailand da kuma na tsakanin kasar Sin da ta kasar Sham. Mun yi haka ne domin horar da 'yan wasa na kungiyar kasarmu, ta yadda za su kara nuna kwarewa a gun gasa. Ban da wadannan kuma, mun yi wasu gwaje-gwaje domin kyautata ayyukan gudanar da harkokin duk birnin da kuma na filin wasannin". Sa'annan Mr. Zhao Qinghua ya bayyana cewa: " Da yake cibiyar wasannin motsa jiki ta Qinhuangdao ta kasance wani filin wasan kwallon kafa na farko da aka kammala gina shi cikin kasar Sin domin taron wasannin Olympic na Beijing, don haka kuwa, akwai wasu abubuwan da za a kyautata su. A lokacin da mataimakin shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa da kasa Mr. Issa Hayatou yake yin ziyarar gani da ido a nan birnin Qinhuangdao, inda shi ma ya gabatar da nasa shawarwari masu kyau. Mr. Zhao Qinghua ya kara da cewa: " Mun kuma yi kwaskwarimar filin wasan daidai bisa bukatun kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing da kuma na wasu hukumomin da abin ya shafa na kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa da kasa".
Jama'a masu sauraro, ko kuna sane da cewa, cibiyar wasan motsa jiki ta Qinhuangdao na da manyan gine-gine guda uku, wato filin wasannin motsa jiki, da dakin wasannin motsa jiki da kuma dakin horar da 'yan wasa. Yanzu, batun yin amfani da ginin cibiyar bayan taron wasannin Olympic na Beijing ya fi janyo hankulan mazauna birnin da yawansu ya kai 440,00 kawai. Game da wannan dai, Mr. Zhao Qinghua ya fadi cewa:
"Lallai mun yi la'akari sosai da wannan batu. Mun gina wani babban kanti a cikin wani ginin dake waje da filin wasannin ; Ban da wannan kuma, mun gina wasu gidaje domin amfanin 'yan kasuwa, wato ke nan za mu bada hayar wadannan gidaje bayan an kawo karshen gasannin.Dadin dadawa, za mu gina wata cibiyar wasan kwallon tennis, da wata cibiyar wasan tseren gudu da takalma masu taya da kuma wasu kananan filayen horaswa na wasan basketball da na bili. Lallai za a mayar da wadannan gine-gine a matsayin wani babban lambun shan iska na wasannin motsa jiki''. ( Sani Wang)
|