
Wakilin gidan rediyion CRI ya ruwaito mana labari cewar, yayin da mataimakin shugaban kwamitin gasar wasannin Olympics ta kasar Girka Isidiris Kouvelos ke zantawa da wakilinmu a ranar 20 ga wata, agogon wurin, ya bayyana cewar, an rigaya an kammala aikin share-fagen bikin kunna wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Mr. Kouvelos ya fadawa wakilinmu cewar, Girka tana share-fage sosai wajen shirya wani gagarumin bikin kunna wutar yola. Ya kuma kara da cewar, kasashen Sin da Girka kasashe ne masu wayewar kai wadanda suke da dadadden tarihi da nagartattun al'adu. Ko shakka babu, bukukuwan mika wutar yola za su daukaka cigaban dangantakar abokantaka dake kasancewa tsakanin kasashen biyu, da sa kaimi ga yaduwar hasashen gasar wasannin Olympics.
Tsawon hanyar da za a bi wajen mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a kasar Girka ya kai kilomita 1528. Za a ratsa adadin yankuna 16, da birane 43 na Girka, ciki har da birane 29 inda za a shirya bikin mika wutar yola. A lokacin, akwai masu mika wutar yola guda 605 wadanda za su halarci bukukuwan mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a kasar Girka.(Murtala)
|