Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-21 16:12:07    
Wakilin gudanarwa na kwamitin gasar wasannin Olympic ya yi adawa da kaurace wa gasar wasannin Olympic

cri
A kwanakin baya, wakilin gudanarwa na kwamitin gasar wasannin Olympic, kuma mataimakin shugaban kwamitin mai kula da harkokin gasar wasannin Olympic na kasar Singapore Mr. Huang Sijin ya bayyana a birnin Lausanne na kasar Switzerland cewa, gasar wasannin Olympic tana da amfani ga ciyar da bunkasuwar zaman rayuwa gaba, shi ya sa, bai kamata a yi adawa da ita ba.

Mr. Ng Ser Miang ya fadi haka ne lokacin da ya dudduba halin da ake ciki na shirya gasar wasannin Olympic na samari a birnin Lausanne. A watan Fabrairu na shekarar da muke ciki, kasar Singapore ta sami damar shirya gasar wasannin Olympic na samari a karo na farko na shekarar 2010.

Ministan mai kula da harkokin bunkasuwar zaman rayuwa, da samari, da kuma wasannin motsa jiki na kasar Singapore Dr. Vivian Balakrishnan ya kuma bayar da sanarwar cewa, yanaadawa da wadansu mutane da suke niyyar kaurace wa gasar wasannin Olympic. Yana ganin cewa, za a bata damar yin cudanya tsakanin juna da fahimtar juna da yawa idan an kaurace wa wasannin Olympic, wannan kuma zai sa wadansu yan wasa da suka yi kokarin cimma burinsu a gasar wasannin Olympic su yi bakin ciki sosai. (Zubairu)