Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-21 15:48:22    
Wasannin Olympics na matsa mini kaimi wajen koyon Turanci

cri

Ko kuna sane da cewa, birnin Beijing, wani tsohon babban birni ne mai wayin kai wanda ke da dadadden tarihi, inda akwai wasu tsoffin gine-gine kamar na fadar sarauta da babbar ganuwa da kuma kananan lunguna da dai sauransu, wadanda suke janyo hankulan matafiya na gida da na waje kwarai da gaske. A albarkacin wannan shekara ta wasannin motsa jiki, masu yawon shakatawa mafi yawan gaske na kiran birnin Beijing a kan cewa " Birnin Wasannin Olympics". Saboda haka ne dai, suke jin mamaki musamman a fannin al'adun wasannin Olympics na birnin Beijing, wadanda kuma suke kishin samun ilimi a fannin gine-ginen wasannin Olympics. Daidai bisa wannan dalili ne, kamfanonin yawon shakatawa daban daban na birnin Beijing suka fi sanya matukar kokari wajen gudanar da harkokin yawon shakatawa a fannin wasannin Olympics a wannan shekara. " A yanzu haka dai, kamfaninmu ya rigaya ya tsara wata hanyar dake shafar wasannin Olympics. Alal misali, hanyar zuwa filin wasannin motsa jiki na kasa mai siffar ' Gidan Tsuntsaye' ko " Bird's Nest", da kuma cibiyar wasan iyo mai siffar " Tafkin Wanka" ko "Water Cube" dake kusa da shi.

Mista Shi Jinyu, wani mai ja-goran shakatawa ne saurayi dake da shekaru 25 da haihuwa. An haife shi a nan birnin Beijing. Yau da shekaru biyu da suka shige, ya samu shiga wani babban kamfanin yawon shakatawa a birnin Beijing a matsayin wani mai ja-goran harkokin balaguro bayan ya kammala karatu a Jami'a.

Tun daga shekarar 2001 har zuwa yanzu, zaman rayuwar mazauna birnin Beijing na shafar wasannin Olympics a fannoni daban-daban, kuma gasar wasannin Olympics da ake share fagenta ta kawo wa Mista Shi manyan sauye-sauye, wanda ya fada wa wakilinmu cewa, tun yana yaro karami, ba shi da sha'awar koyon Turanci sai dai bayan ya shiga Jami'a, inda ya mayar da zama wani mai ja-goran yawon shakatawa a matsayin makasudin aikinsa. Duk da haka, ya tarar cewa,masu yawon shakatawa baki dake zuwan nan birnin Beijing sai kara yawa suke a kowace rana a albarkacin karatowar gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008. Mista Shi Jinyu ya gane cewa, idan yana so ya cimma burinsa na gudanar da sana'ar yawon shakatawa, to wajibi ne ya canza halin da yake nunawa wajen koyon Turanci. Bayan kansa ya waye, sai ya kuduri aniyar kokarin koyon harshen Turanci a duk tsawon lokacin karatunsa a jami'a. Hausawa na kan fadi cewa: " Kwalliya ta biya kudin sabulu". Da yake Mista Shi Jinyu ya gwanance a fannin harshen Turanci, shi ya sa ya sami shiga kamfanin yawon shakatawa da har yanzu yake yin aiki a nan. A yayin da yake waiwayen lamarin, yana mai cewa: " Da babu matsin lamba da na samu daga gasar wasannin Olympics ta Beijing, da babu kwarewar harshen Turanci da nake da ita a yau".

Tun daga karshen shekarar da ta gabata, akwai masu yawon shakatawa baki masu tarin yawa da suka zo nan Beijing, inda suka yi balaguro a fadar sarauta, da gidan ibada na aljanna a Beijing da dai sauan shahararrun wuraren tarihi, musamman ma filaye da dakunan wasannin Olympics. Mista Shi Jinyu ya kara da cewa: " A yanzu haka dai, ma'aikatan kamfaninmu na yawon shakatawa na kokarin koyon harshen Turanci, musamman ma wassu kalmomi a game da wasannin Olympics. Ni kam ina so in bada karin taimako ga wannan gagarumar gasa".

A yayin da yake tabo magana kan gasannin Olympics da za a gudunar a nan Beijing, Mista Shi ya yi farin ciki matuka da fadin cewa: " Lallai ina so in je wuraren gudanar da gasanni don kallonsu da kuma bada kwarin gwiwa ga 'yan wasa. Ni kaina ina mai sha'awar wasan kwallon kafa". ( Sani Wang )