Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-21 15:57:00    
Asalin batun Kosovo

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Nasiru Hassan, mazaunin birnin Maiduguri, jihar Borno, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikarsa, malam Nasiru Hassan ya ce, kwanan nan, na ji ana ta ce-ce-ku-ce a kan Serbia da Kosovo, shin yaya batun yake?

Masu sauraro, gaskiya a kwanan nan, batun Kosovo na daukar hankulan duniya sosai. A ran 17 ga wata, majalisar dokokin Kosovo ta gudanar da taron musamman, inda ta zartas da sanarwar 'yancin kan Kosovo, kuma daga gefe daya ne ta sanar da ballewar Kosovo daga Serbia. To, domin amsa tambayar malam Nasiru Hassan, yanzu bari mu dan bayyana muku asalin batun Kosovo.

Da ma Kosovo wani lardi ne mai cin gashin kansa da ke karkashin mulkin jamhuriyar Serbia ta jamhuriyar tarayyar Yugoslavia. Kashi 90% na mazaunan Kosovo 'yan kabilar Albania ne, a yayin da sauran suka kasance 'yan kabilar Serbia da kuma 'yan kabilar Montenegro.

A tarihi, kakanin kakanin 'yan kabilar Serbia da 'yan kabilar Albania sun taba zama a yankin Kosovo. Bayan yakin duniya na biyu, Kosovo ya zama a karkashin mulkin jamhuriyar gurguzu ta tarayyar Yugoslavia sakamakon shigar Serbia cikin jamhuriyar, kuma a shekarun 1960, Kosovo ta zama wani lardi mai cin gashin kansa.

A shekarar 1991, 'yan kabilar Albania sun gudanar da jefa kuri'ar raba gardama wanda bai sami amincewa daga gamayyar kasa da kasa ba, kuma sun yanke shawarar kafa jamhuriyar Kosovo, har ma a watan Mayu na shekarar 1992, sun gudanar da haramtaccen zabe, inda suka zabi "shugaban jamhuriyar Kosovo" tare kuma da majalisar dokokin da ke kunshe da 'yan majalisa 100. Daga nan kuma, an fara samun mulki biyu a Kosovo, wato gwamnatin da mahukunta Serbia suka nada tare kuma da gwamnati da 'yan kabilar Albania suka zaba. Daga baya, a shekarar 1992, jamhuriyar gurguzu ta tarayyar Yugoslavia ta wargaje, kuma jamhuriyar Serbia da jamhuriyar Montenegro sun hada kansu sun kafa jamhuriyar tarayyar Yugoslavia, a yayin da 'yan kabilar Albania da ke Kosovo suka yi amfani da damar sun sanar da kafuwar jamhuriyar Kosovo, amma duk da haka, gamayyar kasa da kasa ba su ko taba amincewa da wannan "sabuwar kasa" ba.

A watan Maris na shekarar 1999, ba tare da amincewar MDD ba ne, kungiyar NATO ta kai hare-hare na tsawon kwanaki 78 a kan jamhuriyar tarayyar Yugoslavia, bisa dalili na wai magance matsalar jin kai a Kosovo. Sa'an nan, a ran 10 ga watan Yuni na wancan shekara, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lamba 1244, wanda ya sake jaddada mulkin jamhuriyar tarayyar Yugoslavia a kan yankin Kosovo da kuma nemi dukan mambobin MDD da su girmama cikakken mulkin kan jamhuriyar tarayyar Yugoslavia da kuma cikakken yankinta. Bisa kudurin, MDD ta tura tawagar musamman zuwa Kosovo don kula da harkokin yankin, a yayin da sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa da ke karkashin jagorancin kungiyar NATO ke tabbatar da tsaro a yankin.

Amma duk da haka, ba a cimma daidaita matsalar Kosovo ba. Sabo da haka, a watan Nuwamba na shekarar 2005, an fara shawarwari kan makomar matsayin Kosovo. A watan Faburairu na shekarar 2007, manzon musamman na MDD a gun shawarwarin ya gabatar da wani shiri, wanda ya ba da shawarar samun 'yancin kan Kosovo tare da sa ido daga gamayyar kasa da kasa, wanda ya samu kiyewa daga bangren Serbia.

Daga baya, babban sakataren MDD, Ban Ki-mmon ya danka wa tarayyar Turai da Amurka da Rasha nauyin gudanar da sabon shawarwari, kuma a karkashin jagorancinsu ne, Serbia da 'yan kabilar Albania suka gudanar da shawarwari sau da dama kan makomar matsayin Kosovo, amma sabo da babban sabanin ra'ayoyinsu, shawarwarin ya lalace a karshen watan Nuwamba na shekarar bara.

Matsayin Kosovo ba ma kawai na shafar Serbia da 'yan kabilar Albania da ke Kosovo ba, haka kuma yana shafar moriyar Amurka da Rasha da kuma kasashe daban daban na tarayyar Turai. Amurka da yawancin kasashen tarayyar Turai suna nuna goyon baya ga samun 'yancin kan Kosovo, a yayin da Rasha da Spain da Girika da Romania suka nuna rashin amincewa. Bayan da Kosovo ta sanar da 'yancin kanta, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da sanarwa, inda ya jaddada cewa, kafin samun umurnin kwamitin sulhu, tawagar musamman da MDD ta tura zuwa Kosovo za ta ci gaba da gudanar da aikinta bisa kuduri mai lamba 1244.(Lubabatu)