Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-21 13:18:24    
Gwamnatin Brown ta Burtaniya tana kasa tana dabo wajen janye sojojinta daga Iraki

cri

Ranar 20 ga wata, wato daidai lokacin da ake cikar shekaru biyar da kasar Burtaniya ta bi sawun kasar Amurka don kaddamar da yaki a kasar Iraki, firaminista Gordon Brown na Burtaniya ya yi ganawa a Mr. John McCain, dan majalisar dattijai ta kasar Amurke, wanda yanzu haka yake yin ziyara a Londan, inda bangarorin biyu suka dora muhimmanci wajen tattauna batun Iraki.

A gun wani taron manema labaru a aka shirya bayan ganawar, Mr.Mc Cain ya furta cewa, kasar Amurka ta jinjina wa sojojin Burtaniya saboda sadaukarwar da suke ta yi a kasar Iraki. Sa'annan ya fadi cewa, da yake ana rashin samun ci gaba wajen matakan da ake dauka a Iraki, don haka ne dai, jama'ar Burtaniya suke nuna bacin rai na shan kaye. Lallai ya fahimci halin zukatansu. Wassu jaridun kasar Burtaniya sun kebe filaye a shafuffukansu don buga kalaman Mc. Cain.Amma ko kalma ba su buga ba game da batun da firaminista Brown ya yi kan wannan batu. Hakan ya bayyana a fili cewa, Mr. Brown ya yi "shiru" kan batun Iraki da ya fi janyo hankulan jama'ar Burtaniya.

Wassu manazarta sun bayyana ra'ayoyinsu cewa, ra'ayin yin shiru da Mr. Brown ya dauka ya shaida cewa Mr.Brown ya shiga tsaka mai wuya. Ana ganin cewa, a zahiri dai, babu bambanci tsakanin Mr. Brown da Mr.Tony Blair kan manufofin da gwamnatin Burtaniya ke aiwatarwa game da harkokin Iraki. Tuni kafin Mr. Brown ya kama mukamin firaminista, ya taba zama ministan kudi na gwamnatin Blair; Ban da wannan kuma, ya taba nuna tsayayyen goyon baya ga Blair yau da shekaru biyar da suka gabata wajen aikewa da sojoji zuwa Iraki. Sai dai bayan da Mr. Blair ya sauka daga mukaminsa cikin halin bacin rai ne Mr. Brown ya wayi gari cewa, batun Iraki, wani batun siyasa ne da ba zai kyale shi ba a kokarinsa na shawo kan jama'ar kasar. Amma duk da haka, bai taba kuduri aniyar ko zai janye sojojin kasar daga Iraki ba tun bayan da ya hau kan kujerar mulki. Bisa kididdigar da aka yi an ce, tun da barkewar yakin Iraki har yanzu, akwai sojoji 175 na kasar Burtaniya da suka rasa rayukansu, kuma yawan kudin da aka kashe a fannin yakin ya kai fam biliyan shida, wato ke nan matsakaicin yawan kudin da kowane dan Burtaniya mai biya haraji ya dauka ya kai sama da fam dari. A yayin da ake yi tambaya a kan cewa "Wane abu ne muka samu daga yakin Iraki", gwamnatin Burtaniya ta gagara wajen bada amsa da ka iya gaskanta mutae.

Tare da karatowar ranar tunawa da cika shekaru biyar da aka kaddamar da yaki a Iraki, jam'iyyu masu adawa da kuma ra'ayoyin bainal jama'a na kasar Burtaniya suna ta yi wa gwamnatin kasar matsin lamba don ta gudanar da bincike kan dalilin shiga yakin Iraki da Burtaniya ta yi da kuma sakamakon lamarin. Bisa wannan yanayi ne, Mr. Brown ya sha alwashi a ran 17 ga wata cewa za a gudanar da bincike kan lamarin duk da cewa a ganinsa lokaci bai yi ba tukuna sakamakon tabarbarewar halin tsaro dake kasancewa yanzu a kasar ta Iraki.

Wassu kwararru a fannin harkokin waje sun yi hasashen cewa, akwai dalilai guda biyu da suka sa gwamnatin Brown ta dauki irin wannan ra'ayi na yin "shiru". Dalili na farko shi ne, Jam'iyyar Labou Party da shi Mr. Brown sun samu durkushewar kwarjininsu kuma magoya bayansu suna baya-baya na Jam'iyyar Conservative Party tun bayan da Mr. Brown ya karbi mulki daga hannun Mr. Blair a watan Yuni na shekarar bara saboda gwamnatinsa ta yi kurakurai iri daban-daban lokacin da take gudanar da harkokin gida na kasar. Saboda haka ne, Jam'iyyar Labour Party da Mr. Brown suka samu rashin tabbaci ga canja irin wannan yanayi maras kyau yayin da suke yin amfani da batun Iraki; Dalili na biyu shi ne, idan yanzu kasar Burtaniya ta janye sojojinta daga Iraki, to labuddah hakan zai haifar da tsaiko ga kasar Amurka. Shugaba Bush na Amurka ya aike da Mc.Cain zuwa Burtaniya domin yin ziyara daidai a albarkacin ranar cika shekaru biyar da aka tayar da yakin Iraki, wannan dai ya bayyana yadda kasar Amurka ke damuwa da lamarin. ( Sani Wang)