Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-20 20:10:11    
Kasar Sin tana fatan kasashen duniya ba za su goyi bayan Dalai Lama da aikace-aikacensa na kawo baraka ba

cri
Ran 20 ga wata, a nan Beijing, Qin Gang, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan kasashen duniya za su gane ainihin burin Dalai Lama, wato yana neman kawo wa kasar Sin baraka, kuma ba za su nuna masa goyon baya da kuma mara masa baya wajen gudanar da aikace-aikacen kawo baraka ta ko wace hanya ba.

A wannan rana, a gun taron manema labaru da ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta saba shiryawa, Mr. Qin ya ce, mummunan tashin hankali da aka samu a kwanan baya a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin ya sake bayyana ainihin burin rukunin Dalai Lama, wato yana ta neman kawo wa kasar Sin baraka. Dukkan yunkurin lalata kwanciyar hankali na zaman al'ummar kasa da kawo wa kasar Sin baraka ba za su sami amincewa daga jama'a ba, haka kuma, tabbas ne za su ci tura.

Wannan kakaki ya ci gaba da cewa, gwamnatin Sin tana sauke nauyi bisan wuyanta. Kullum tana dukufa wajen samun zaman lafiya da bunkasuwar duniya. Ko wace kasa a duniya ba ta amince da kasancewar gwamnatin Tibet ta wai da ke gudun hijira ba. Sa'an nan kuma, dukkan kasashen duniya na tsayawa tsayin daka kan bunkasa huldar hadin gwiwa da abokantaka a tsakaninsu da Sin.(Tasallah)