Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-20 19:52:31    
Ana share fagen aikin mika yolar gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing bisa shirin da aka tsara

cri

Yau, wato ran 19 ga wata, kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing ta shekarar 2008 ya bayyana cewa, ana share fagen aikin mika yolar Olympics bisa shirin da aka tsara. A ran 24 ga watan Maris ne za a kunna yolar Olympics a kasar Greece

Mr. Jiang Xiaoyu, mataimakin shugaban kwamitin ya bayyana cewa, yanzu an riga an tabbatar da hanyar mika yolar da za a bi. A waje daya kuma, ana zabi mutane wadanda za su mika yola kamar yadda ya kamata. Ya zuwa yanzu, an riga an kammala aikin zaben mutanen da za su mika yola a yankuna da kasashe 16, kuma sun riga sun gabatar da takardar sunayensu.

Bisa shirin da aka tsara, za a shirya bikin daukar wuta mai tsabta domin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing a garin Olympia na kasar Greece. Sannan za a mika wannan wutar yola a kasar Greece har na tsawon kwanaki 6. A ran 31 ga watan Maris, za a iso da wutar yolar mai tsabta a nan birnin Beijing. Tun daga ran 1 ga watan Afrilu, za a soma mika wutar yolar mai tsabta a nan kasar Sin da a sauran kasashen duniya. A ran 8 ga watan Agusta da dare, za a iso da wutar yola mai tsabta a gun bikin kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing. (Sanusi Chen)