Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-20 19:21:13    
Wasu kasashe sun yi adawa da kaurace wa wasannin Olympics na Beijing saboda batun Tibet

cri

A kwanakin baya, wasu kasashe sun nuna cewa suna adawa a kaurace wa wasannin Olympics na Beijing ta hanyar yin amfani da batun Tibet, kafofin watsa labaru na kasashe dabam daban sun lura da haka sosai.

A ran 19 ga wata a Islamabad, babban birnin kasar Pakistan, Mr. Haque ministan harkokin waje na kasar ya gana da Mr. Luo Zhaohui jakadan kasar Sin, ya ce, a kwanakin baya, wasu mutane sun yi al'amarin ta da manyan laifuffuka masu tsanani sosai a lardin Tibet na kasar Sin domin neman lalata cikakken yankin kasar Sin da wasannin Olympics na Beijing, gwamnatin kasar Pakistan ta yi kakkausar suka ga wannan. Ya ce, wasannin Olympics shi ne wani biki na dukkan jama'ar kasashen duniya, idan aka lalata wasannin Olympics na Beijing, to ba za a yi hasara ga jama'ar kasar Sin kawai ba, har ma za a yi hasara ga dukkan jama'ar duniya.

Game da "kaurace wa wasannin Olympics na Beijing" da aka gabatar saboda batun Tibet da batun hakkin 'dan Adam, a ran 20 ga wata, Mr. Havey mataimakin hukumar shirya wasannin Olympics na kasar Australia ya ce, ko wane irin aikace-aikacen kaurace wa wasannin Olympics zai zama shirme. Ya yi imanin cewa, za a yi wasannin Olympics na Beijing yadda ya kamata.