Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-20 18:03:18    
Mutane wadanda suka samu hasara ko suka ga yadda aka yi tashin hankali a Lhasa a idanunsu sun bayyana abubuwan da suka gani

cri
A kwanan baya, wasu tsirarrun masu bin addinin Buddha na dakunan ibada da ke cikin birnin Lhasa na jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin sun taru sun ta da hankali a birnin, kuma sun lalata zaman doka da oda na al'ummar birnin Lhasa sosai, kuma sun haddasa babbar hasara ta rayuka da dukiyoyin jama'ar birnin. Bayan aukuwar matsalar, gwamnatin jihar Tibet ta dauki matakan halal ba tare da bata lokaci ba domin yaki da manyan laifuffukan nuna karfin tuwo. Yanzu an riga an kwantar da kura a birnin Lhasa kamar yadda ya kamata. Yanzu ga wani bayani game da yadda aka yi wannan tashin hankali mai tsanani a birnin Lhasa da mutane wadanda suka samu hasara ko suka ga yadda aka yi wannan tashin hankali a idanunsu sun bayyana mana.

Lokacin da yake tunawa da abubuwan da ya gani a wancan rana, Mr. Nyima Tsering, shugaban makarantar firamare ta Haicheng da ke birnin Lhasa ya ce, lokacin da dalibai suke komawa makarantar bayan cin abincin rana, masu laifuffuka sun kai farmaki kan makarantarsa. Mr. Nyima Tsering ya ce, "wadannan masu laifuffuka sun kai farmaki kan makarantarmu kamar yadda mahaukata suke yi. Sun kawo barazana sosai ga lafiyar dalibai da malamai da dukiyoyin makarantar. A cikin irin wannan hali mai tsanani da muke ciki, nan da nan ne malamai sun mai da dukkan dalibai cikin ajinsu domin tsaronsu, kuma sun sanar wa iyalansu cikin lokaci domin tabbatar da ganin iyalai sun mai da yaransu gidaje lami lafiya. Yawan hasarar da aka kawo wa makarantarmu sakamakon wannan matsala ya kai kudin Sin yuan miliyan 1 da dubu dari 4. Amma abu mafi tsanani shi ne ta kawo illa sosai ga zuciyar dalibanmu."

Misalin karfe 11 na ran 14 ga watan Maris da safe, wasu masu bin addinin Buddha sun soma yin amfani da duwatsu domin kai farmaki kan 'yan sanda wadanda suke sintiri a kan titunan da ke dab da dakin ibada na Ramoche kamar yadda suka saba yi a kowace rana. Daga baya, wasu 'yan ta'adda sun soma taruwa a kan tituna, kuma suna kururuwar kawo wa kasar Sin baraka, kuma sun soma buga mutane da kwace kayayyaki daga kantuna da kona gine-gine na makarantu da asibitoci da bankuna da kafofin yada labaru da suke manyan tituna na birnin Lhasa.

Lokacin da take tunawa da matsalar da ta gani a wannan rana, yarinya Dawa Yudron, wadda take karatu a aji na 4 na matakin 2 a makarantar firamare ta Haicheng tana jin tsoro sosai har yanzu, ta ce, "Na ga wasu mutane suna buga 'yan sanda, wasu suna farfashe kantuna. Ina jin tsoro sosai. Kakata ta nemi da kada na koma makaranta. Sabo da haka, na zauna a gida har kwanaki 3."

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan gidajen jama'a da kantunan da 'yan ta'adda suka kona ya kai fiye da 210, kuma sun lalata da kona motoci 56. Kuma sun kashe da kuma kona mutane fararen hula 13 a cikin wannan matsala. A wani asibitin Lhasa, wakilinmu ya gana da Peng Xiaobo wanda ya ji rauni a cikin matsalar. Ya ce, 'yan ta'adda sun yi amfani da man fetur sun kona kantunansa hudu. Lokacin da ake tashin hankali, Peng Xiaobo da iyalansa 3, wato matarsa da wani kawunsa da wata kanwarsa suna son tsalle daga bene na biyu domin neman tsirar da su da kansu. Amma matarsa ta ji rauni sosai. Kuma an kona kawunsa da kanwarsa da rayukansu, sun mutu domin ba su iya tsirar da su daga gidan da aka kunna ba. Lokacin da yake tunawa da wannan matsala, Mr. Peng ya nuna bacin rai kuma ya yi kuka sosai. "Ina da wata kanwa mai shekaru 18 da haihuwa kawai. A wancan lokaci, ba zato ba tsammani 'yan ta'adda sun kona dukkan gidanmu mai hawa biyu. Kanwata ta ji tsoro, ba ta tsalle daga taga ba, tana son gudu daga tsani, amma an riga an kunna wannan tsani. Daga karshe dai an kunna kanwata da rai, kanwata ta mutu."