Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-20 17:01:55    
Matasa na babban yanki da na Taiwan na kasar Sin suna fatan isowar wasannin Olympics

cri

Nan da ba da dadewa ba samari sama da dari hudu na babban yanki da na Taiwan na kasar Sin sun hallaru a nan birnin Beijing,sun ziyarci dakunan wasannin Olympics na Beijing da Babbar Ganuwar kasar Sin,sun je muhimmin filin wasanni inda aka gina wani babban gini da sifarsa tamkar shekar tsuntsaye da tsohun wurin lambun shan iska na Yuanminyuan.samari na bangarori biyu ba su dauki kansu a matsayin 'yan kallo ba kan wasannin Olympics na Beijing.

Mr Zang Peng wanda ya zo daga jami'ar Beijing wadda ta fi shahara a kasar Sin ya gaya wa wakilimmu cewa,shi dan sa kai ne ga wasannin Olympics na birnin Beijing a shekara ta 2008,shi kuma mai tafinta ne a wasannin Olympic na Beijing,zai ba da hidima wajen fassara da turanci a fanning kiwon lafiya.Wannan ne ba karo na farko ba ne da samari na babban yanki da na Taiwan sun hallaru.Bayan da suka yi taruwa,su koma makarantunsu.Da ya koma makaranta ya kan yi hira da abokai sabbi da tsaffi ta yanar gizo ta internet."Duk lokacin da muka taru,na kan yi hira da su cikin dogon lokaci.dukkamu samari ne,watakila muna da ra'ayin daban daban,duk da haka mun yi farin ciki da ganin juna cikin wannan taruwa.ta haka kuwa mu kara kusantar juna."

A nan birnin Beijing,samarin da suka zo daga babban yankin kasa da na Taiwan sun saurari bayyanan da tsohon mataimakin shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Sin Mr Wei Jizhong da mataimakin shugaban kwamitin zartaswa na kungiyar shirya wasannin Olympics na Beijing Mr Jiang Xiaoyu suka yi kan tarihin kasar Sin kan wasannin Olympics da yadda birnin Beijing ta nemi samu damar shirya wasannin Olympics da kuma ci gaban da aka samu wajen shirya wasannin Olympic na birnin Beijing.Sun ziyarci dakunan wasannin Olympics dake cikin ginawa.Dukkan samari sun yi alfahari da wasannin Olympic a mahaifarsu.Da suka shiga sabbin filayen wasanni,kowa na cike da fara'a.A wata rana a dakin wasannin Olympics dake Wukesong na birnin Beijing sun kallaci gasar gwaji ta wasan kwallon baseball,samarin babban yankin kasar ba su da isashen ilimi kan wannan wasa,sai samarin da suka zo daga Taiwan sun kara musu ilimi.dukkansu sun yi tafi tare da kara wa kungiyar Sin kuzari.

Da wakilinmu ya gana da Mr Hong Ruting,dalibi na jami'ar samar da ilimi ta Taipei,ya yi hira da wani sabon aboki na babban yankin kasa kan wasan baseball.Ya yi farin ciki sosai da samu damar farko ta kallon wasa a cikin sabon dakin wasannin Olympic na birnin Beijing da aka gina.Ya kawo wasu shawarwari kan sabon dakin wasan"Wata rana da na yi kallon wasa a sabon daki,na ga a gefuna uku dake kewayen fili da akwai kujeru,a ganina a nan birnin Beijing kamata ya yi a kara kujeru.a filin wasan baseball na Taiwan an kewaye shi da kujeru,ina fatan a kewaya filin Beijing da kujeru.

Kusan dukkan matasa suna so su zama masu sa kai ga wasannin Olympics na birnin Beijing,Miss Zeng Shuya,daliba ce da ta zo daga lardin Taiwan,yanzu take kararu a jami'ar koyon ilimin likitancin kasar Sin na gargajiya,ta yi bakin ciki da gaza zama 'yar sa kai ga wasannin Olympic na birnin Beijing."A hakika dai ni ma na sani ina makara.da na sami labari ana daukar ma'aikata masu sa kai ga wasannin Olympic na Beijing,sai na je ofishin kula da harkokin Hongkong da Macao da na Taiwan in yi rajista,sai sun ce jeren sunayen ya cika."

Cikin dogon lokaci,samari na babban yankin kasa sun kara saninsu game da Taiwan ne ta kafofin yada labarai kamar su telebiji da yanar gizo ta internet.A wannan karo sun hallaru gu daya sun yi mu'amala kai tsaye,sun zauna tare sun yi hira yadda suka ga dama,ta haka aka kara kusantar juna tsakaninsu.

Miss Zhang Yuxi,wata daliba ce da ta zo daga jami'ar koyon ilimin wasanni ta birnin Beijing,budurwa ce mai fara'a.Ta yi farin ciki da ganin aminanta na Taiwan sun fi son kallon wasannin telebiji da ganin tarmamuwa wadanda suka fi shahara a fanning wasannin. Ta ce A ganina babu bambancin dake tsakanin mutanen Taiwan da na babban yankin kasa,muna da ra'ayoyin bai daya a kan fannoni da dama.Muna iya tattauna kome da kome ciki har da batun tamamuwa ko wane ne shi ne tarmamuwa.samarin Taiwan sun fi so kallon wasannin telebiji na babban yankin kasa kamar "nagartattun maza" da "muryar superwoman".wasannin Taiwan ma sun samu karbabuwa a babban yankin kasa.

Bayan da suka sauka a babban yankin kasa,samarin da suka zo daga lardin Taiwan sun sha bayar da ra'ayinsu cewa cigaban mahaifar kasa ya bude idanunsu.Madam Liu Hua,shehun mallama ta sashen wasanni na jami'ar fasaha ta Taiwan ta ce "Ina fatan za a yi muamala tsakanin bangarori biyu a fanning al'adun wasanni.Ni mai koyon ilimin wasanni ce,ni kuma mai shirya wasanni ce ina so in shirya wasan gabatarwa.ni ma ina sha'awar wasannin motsa jiki.ziyararta a babban yankin kasa ta bude idanuna.duniya daya buri daya."

A cikin taruwa ta kwanaki uku kawai,samari na babban yankin kasa da na Taiwan sun kulla zumunci mai zurfi,wsannin Olympics na birnin Beijing a shekara ta 2008 ne ya dauke hankulanmu gaba daya.Da muryar Deng Yaping,yar wasan Olympics a matsayin farko a duniya ya kawo karshen bayanin da wakilinmu ya rubuta"A ganina kakani kakaninmu daya ne,dukkanmu muna da burin shirya wasannin Olympic na tsawon shekaru dari,kamata ya yi mu samari mu dauki nauyi a bisan wuyanmu domin gwada halin al'ummar kasar Sin.