Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "ilmin zaman rayuwa". Ni ce Kande ke jan akalar shirin. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku wani bayani kan kiwon lafiyar tsofaffi.
Kwararru masu ilmin aikin likitanci na kasar Amurka sun gudanar da wani bincike ga tsofaffi wajen dangantakar da ke tsakanin kayayyakin lambu da tabarbarewar kwakwalwa, daga baya kuma sun gano cewa, kara cin kayayyakin lambu zai ba da taimako wajen hana tabarbarewar kwakwalwa, ta yadda za a iya saukake lalacewar tunani wanda tabarbarewar kwakwalwa ke haddasawa.
Manazarta na jami'ar Rush da ke birnin Chicago na kasar Amurka sun buga wani labari a kan mujallar ilimin nazarin jijiyoyin dan Adam, inda suka nuna cewa, sun gudanar da wani bincike na tsawon shekaru shida ga tsafaffi maza da mata 2000 wadanda shekarunsu ya zarce 65 da haihuwa kan abincin da su kan ci. Daga baya kuma sun gano cewa, tabarbarewar kwakwalwar tsofaffin da su kan ci kayayyakin lambu a ko wace rana ta ragu da kashi 40 cikin dari idan an kwatanta da wadanda ba su ci kayayyakin lambu ko kadan ba.
A cikin kayayyakin lambu iri daban daban, wadanda suke da koren ganye sun fi ba da kariya ga lafiyar dan Adam. Manazarta sun bayyana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da kayayyakin lambu da ke da koren ganye suna kunshe da bitamin E mai yawa wanda zai ba da taimako sosai ga lafiyar jikin dan Adam. Ana ganin cewa, bitamin E yana iya taimakawa wajen hana lalacewar kwayoyin jikin dan Adam, ta yadda zai iya saukaka cutar tabarbarewar kwakwalwa.
Malam Claire Mirrlees, mai kula da wannan bincike ya bayyana cewa, 'ya'yan itatuwa su ma suna kunshe da bitamin E, amma ya yi kadan idan an kwatanta shi da wanda ke cikin kayayyakin lambu. Bugu da kari kuma, cin kayayyakin lambu bayan da aka dafa su tare da man zaitun zai ba da taimako ga jikin dan Adam wajen karbar bitamin E. Haka zalika kuma kitsen da ke cikin man kayan lambu zai ba da taimako wajen rage yawan kitsen da ke taruwa a jijiya, wanda ke hana jini gudu, ta yadda za a ba da taimako wajen kiyaye lafiyar kwakwalwa.
Ma'anar abinci irin na Bahar Rum ita ce abincin da 'yan kasashen da ke bakin Bahar Rum su kan ci a zaman yau da kullum, wanda yawancinsu shi ne kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa da kifaye da wake da kuma man zaitun.
Bisa bayanin da kafofin watsa labarai na kasar Birtaniya suka bayar a kwanan nan, an ce, manazarta na jami'ar Cambridge ta kasar Birtaniya da kuma cibiyar nazari kan sankara ta kasar Amurka sun gudanar da bincike ga 'yan kasashen biyu fiye da dubu 560 da shekarunsu ya kai daga 50 zuwa 71 da haihuwa. Daga baya kuma manazarta sun yi nazari kan mutanen da suka ci dimbin kayayyakin lambu da wake da 'ya'yan itatuwa da ire-iren 'ya'yan itatuwa da hatsi da kifaye da kuma nama a cikin shekaru biyar da suka gabata, kuma sun gano cewa, yawan mutuwar mutanen da su kan ci abinci irin na Bahar Rum ya samu raguwa. Yiyuwar mutuwar maza sakamakon cututtukan zuciya da hauhawar jini ta ragu da kashi 22 cikin dari, kuma yiyuwar mutuwar maza sakamakon sankara ta ragu da kashi 17 cikin dari. Haka kuma yiyuwar mutuwar mata sakamakon cututtukan zuciya da hauhawar jini ta ragu da kashi 21 cikin dari, yiyuwar mutuwar mata sakamakon sankara ta ragu da kashi 14 cikin dari.
|