Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-19 16:29:06    
Darakta mai martaba na kwamitin bada shawara kan harkokin raya jihar Tibet mai cin gashin kanta ya la'anci yunkurin lalata zaman lafiya a jihar

cri
Wakilin gidan rediyon CRI ya ruwaito mana labari cewar, yau 19 ga wata a nan birnin Beijing, da kakkausan harshe ne, wani mai fadi-a-ji na kabilar Tibet, kuma darakta mai martaba na kwamitin bada shawara kan harkokin raya jihar Tibet mai cin gashin kanta Mr. Ragdi ya yi Allah wadai da dukkan miyagun laifuffukan da aka aikata na tada tarzoma a babban birnin Tibet wato Lhasa, inda aka yi duke-duke, da fasa kayayyaki, da kwace kayayyaki da cunnawa abubuwa wuta.

Kwanakin baya, wato ranar 14 ga wata, tsirarrun mutane sun tattaru a Lhasa, inda suka yi duke-duke, da fasa kayayyaki, da kwace kayayyaki, tare kuma da kone abubuwa. Sakamakon haka, gidajen kwana da shaguna sama da 210 an kone su, haka kuma, an lalata da cunnawa motoci wuta da yawansu ya kai 56, da konewa ko sassara fararen hula gunduwa-gunduwa da yawansu ya kai 13.

Mr. Ragdi ya yi nuni da cewar, gungun mutane mabiya Dalai Lama 'yan a-ware dake ketare ne suka tayar da wadannan al'amuran tashe-tashen hankula da gangan, wadanda suka lalata doka da oda ta zamantakewar al'umma. Haka kuma, wadannan miyagun laifuffukan da suka barkata sun kawo babbar hasara ga zaman rayuwar jama'a da dukiyoyinsu, kuma sun yi zagon-kasa ga doka da oda da kwanciyar hankali a zamantakewar al'ummar Tibet. Ya kuma kara da cewar, wadannan munanan al'amuran sun sake shaida cewa, gungun mutane mabiya Dalai Lama ba su daina danyen aikinsu ba na yunkurin kawowa kasar Sin baraka. Makasudinsu shi ne tada tarzoma a wannan muhimmin lokaci, a wani yunkurin yin zagon-kasa ga gasar wasannin Olympics, da lahanta zaman lafiya da zaman jituwa a nan kasar Sin.

Kazalika kuma, kwanan baya, wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya sun karawa labari gishiri, sun maida miyagun laifuffukan tada tarzoma tamkar zanga-zangar nuna adawa cikin ruwan sanyi. Game da haka, Mr. Ragdi ya bayyana cewar, ko shakka babu, duk wata kasa da gwamnati a duniya za ta dauki tsauraran matakai domin kiyaye zaman rayuwar jama'a da dukiyoyinsu, idan akwai tashe-tashen hankula kamar irinsu a Lhasa.(Murtala)