Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-19 16:16:19    
Kwamitin shirya gasar wasannin Olmpic ta Beijing ya fara dudduba filaye da dakunan wasannin Olympic

cri

Tun daga karshen mako nan, hukuma mai kula da harkokin filin wasa da dakin wasa na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic a karo na 29 za ta fara dudduba filaye da dakunan wasanni dake Beijing bi da bi, don tabbatar da samun kyakkauwan halin filaye da dakunan wasannin Olympic.

Mai taimakin shugaban hukumar kula da harkokin filaye da dakunan wasanni na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing Mr. Yao Hui ya fadi haka ne lokacin da ya gana da wakilinmu a ran 19 ga wata a birnin Beijing. Ya bayyana cewa, za a ci gaba da gudanar da aikin nan zuwa watan Yuni, ayyukan da za a dudduba, sun hada da aikin gine-gine kayayyakin filaye da dakunan wasanni, da kwarewar wadansu mutane masu aiki a can, da dai sauransu. Ban da wannan kuma, Mr. Yao Hui ya kara da cewa, nan gaba, wadansu hukumomin da abin ya shafa za su dudduba ingancin filaye da dakunan wasanni na Beijing da kuma aikin kiwon lafiyarsu. (Zubairu)