Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-19 14:10:12    
A galibi dai kura ta lafa a birnin Lhasa na jihar Tibet

cri

Wakilinmu ya ruwaito mana a ran 18 ga wata cewa, a cikin muhimman unguwanni da tituna na birnin Lhasa na jihar Tibet mai cin gashin kanta, motoci suna tafiye-tafiye cikin 'yanci, galibin kantuna sun farfado da aikinsu, daliban jami'o'i da na sakandare da na firamarori sun yi karatu yadda ya kamata, a galibi dai, an riga an farfado da tsarin zaman al'ummar birnin Lhasa.

A ran 14 ga wata, bayan da wasu 'yan tsirarun mutane suka tada mummunan tashin hankali a birnin Lhasa, gwamnati da hukumomin da abin ya shafa na wurin sun yi hakuri kuma sun kwantar da tarzoma. Daga ran 17 ga wata, muhimman gwamnatoci da hukumomi da kamfannoni na birnin Lhasa da na jihar Tibet sun farfado da aiki kamar yadda ya kamata.

A ran 18 ga wata da safe, wakilinmu yana ganin cewa, yawan mutane da motoci a kan tituna ya karu a zahiri, bos da taxi da kekuna suna tafiya yadda ya kamata. Kasuwannin samar da kayayyaki sun samu farfadowa bi da bi. Yanzu, jiragen kasa da jiragen sama da motoci masu tafiya na dogon zango da na gajeren zango suna zirga zirga yadda ya kamata a birnin Lhasa.(Lami)