Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-19 09:17:09    
Gasar cin kofin duniya cikin daki ta bincika sakamakon horon da ake yi wa 'yan wasan tsalle-tsalle da guje-guje na kasar Sin domin shiga gasar wasannin Olympic

cri

A gun gasar cin kofin duniya ta wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta shekarar 2008 da aka shirya a cikin daki kwanakin baya ba da dadewa ba, 'yan wasan kasar Sin sun samu lambar zinariya daya da lambar tagulla daya, wannan shi ne sakamako mafi kyau da 'yan wasan kasar Sin suka samu a gun wannan gasa a cikin shekaru wajen 20 da suka gabata. Kamar yadda kuka sani, za a yi gasar wasannin Olympic a birnin Beijing bayan watanni biyar, shi ya sa, ana iya cewa, wannan gasar cin kofin duniya cikin daki ta bincika sakamakon horon da ake yi wa 'yan wasan tsalle-tsalle da guje-guje na kasar Sin. A cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku bayani kan wannan.

A watan Maris na wannan shekara, aka shirya gasar cin kofin duniya ta wasannin tsalle-tsalle da guje-guje cikin daki ta shekarar 2008 a birnin Valencia na kasar Spain, wannan gasa ita ce gasar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta farko mafi muhimmanci a duniya a wannan shekara, daga baya 'yan wasa fiye da 600 da suka zo daga kasashe da shiyoyyi 119 sun hallarci gasar. 'Yan wasa 11 na kungiyar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta kasar Sin sun shiga gasa hudu na maza da kuma na mata. A cikinsu, 'dan wasa Liu Xiang ya fi jawo hankulan mutanen duniya. A gun gasar gudun tsallake shinge na mita 60 na maza, Liu Xiang ya samu zama na farko da dakika 7 da 46, ya samu lambar zinariya daya tak ta kasar Sin, daga nan kuma, Liu Xiang ya samu nasarar zama zakara na gudun tsallake shinge na maza na gasar wasannin Olympic da gasar cin kofin duniya a wajen daki da gasar cin kofin duniya a cikin daki da kuma matsayin koli na duniya.

Ba ma kawai a cikin gida kasar Sin, har ma a kasashen waje, a kullum Liu Xiang ya fi jawo hankulan 'yan kallon wasa. Dalilin da ya sa haka shi ne domin sakamako mai faranta ran mutane da Liu Xiang ya samu. Ko irin wannan hali zai matsa masa lamba? Game da wannan , Liu Xiang ya ce:  "Ba damuwa, zan ci gaba da yin kokari, a da, na taba samun zakaran wasannin Olympic, zakara ba abu mafi muhimmanci ba ne, amma zan yi kokari."

Ban da wannan kuma, sauran 'yan wasan tsalle-tsalle da guje-guje na kasar Sin su ma sun samu sakamako mai gamsarwa a gun gasar, alal misali, 'yar wasa ta kasar Sin Li Meiju ta samu lambar tagulla ta gasar jefa kwallon darma ta mata, 'dan wasa Shi Dongpeng ya samu zama ta 9 ta gasar gudun tsallake shige na mita 60 na maza a cikin gasar mataki na biyu. Dukkan wadannan sun nuna mana cewa, 'yan wasan tsalle-tsalle da guje-guje na kasar Sin suna daga matsayinsu a kai a kai yayin da suke yin horo domin shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Babban malamin koyar da wasa na kungiyar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta kasar Sin Feng Shuyong ya ce, daga sakamakon gasa, ana iya gane karancin horo, shi ya sa ana iya cewa, gasar cin kofin duniya ta wasannin tsalle-tsalle da guje-guje cikin daki ta shekarar 2008 ta bincika sakamakon horon da ake yi wa 'yan wasan kasar Sin. Ya ce : "A takaice dai, daga sakamakon gasar, ana iya gane ainihin halin da muke ciki, wato kamata ya yi mu ci gaba da yin kokari."

A watan Agusta na bana, za a fara gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008 a birnin Beijing, shi ya sa a gun gasar cin kofin duniya ta wasannin tsalle-tsalle da guje-guje cikin daki ta shekarar 2008, 'yan wasan kasashen duniya sun bincika sakamakon da suka samu bayan suka yi horo cikin dogon lokaci, kungiyar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta kasar Sin ita ma haka ne. Babban malamin koyar da wasa Feng Zhuyong yana ganin cewa, bayan aka kammala wannan gasa, kungiyar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta kasar Sin ta kara gane matsayinta a duniya. Ya ce :  "Ana iya cewa, wannan gasa ita ce gasa mai matsayin koli ta karshe da aka shirya kafin gasar wasannin Olympic ta Beijing, sakamakon gasar ya nuna mana cewa, matsayin wasannin tsalle-tsalle da guje-guje na kasar Sin ya kai matsayin matsakaita a duniya kawai, shi ya sa dole ne mu kara yin kokari kafin gasar wasannin Olympic ta Beijing." (Jamila Zhou)