Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-19 09:15:20    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (12/03-18/03)

cri

Ran 13 ga wata, agogon wurin, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasar Greece Minos Kyriakou ya shirya taron watsa labarai inda ya sanar da cewa, 'dan wasan karate na kasar Greece Alexandros Nikolaidis wanda ya taba samu lambar azufa ta gasar wasan karate ta aji kilo 80 a gun gasar wasannin Olympic ta Athens zai zama mai mika wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing na farko a cikin yankin kasar Greece, kuma 'yar wasan tsallen nesa na yin dira 3 ta kasar Greece wadda ta taba samu lambar azurfa a gun gasar wasannin Olympic ta Athens Pigi Devetzi za ta zama ta karshe. Bisa shirin da aka tsara, a ran 24 ga wata, da misalin karfe 12, agogon wurin kasar Greece, za a karbi wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a tsohon wurin Olympia, daga baya kuma, jerin motoci wanda ke kunshe da motoci 14 zai tsaron masu mika wutar yula 650 da su mika wutar yula a cikin yankin kasar Greece, gaba daya tsawon tafiyarsu zai kai kilomita 1528, kuma za su kwashe kwanaki 7. A ran 30 ga wata, da misalin karfe 3 da yamma, za a isar da wutar yula a filin gasar wasannin Olympic ta zamani ta farko ta shekarar 1896 dake cibiyar birnin Athens. Kwamitin wasannin Olympic na kasar Greece zai yi bikin taya murna a nan kuma zai mika wa kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing wutar yula.

Ran 16 ga wata, agogon wurin, aka kammala gasar wasan kwallon badminton ta matsayin koli ta shekarar 2008 a kasar Switzerland, 'dan wasan kasar Sin Lin Dan ya lashe 'dan wasa daga kasar Malaysia Li Zongwei ya samu zama ta farko ta maza, 'yar wasa ta kasar Sin Xie Xingfang ta lashe 'yar wasa daga kasar Sin Zhang Ning ta samu zama ta farko ta mata. Ban da wannan kuma, 'yan wasan kasar Sin sun samu zakaru na gasar gaurayen namiji da mace da kuma zakaru na gasa tsakanin mata biyu biyu.

Ran 16 ga wata, agogon wurin, a birnin Seoul na kasar Korea ta kudu, a gun gasar gudun dogon zango wato Marathon ta duniya ta shekarar 2008, 'yar wasa daga kasar Sin Zhang Shujing ta samu zama ta farko ta mata da awa 2 da minti 26 da kuma dakika 11. Wannan a karo na uku ne da ta samu zama ta farko ta gasar gudun dogon zango wato marathon da aka shirya a birnin Seoul na kasar Korea ta kudu. Ban da wannan kuma 'yar wasa daga kasar Sin Wang Xueqing ta samu zama ta biyu.(Jamila Zhou)