Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-18 21:20:36    
Kasar Sin ta bayyana ra'ayinta game da sanarwa Eu kan batun Tibet

cri
Ran 18 ga wata, a nan Beijing, Qin Gang, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin Sin tana fatan kungiyar tarayyar Turai wato EU za ta girmama abubuwan gaskiya, za ta bambance abubuwan gaskiya, za ta kuma yi hadin gwiwa da kasashen duniya domin hana laifuffukan rukunin Dalai tare.

Qin ya fadi haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin da manema labaru suka yi masa game da lamarin. Ya kuma kara da cewa, gwamnatin Sin ta lura da cewa, kungiyar EU ta ba da wata sanarwar shugaba kan halin da ake ciki a jihar Tibet mai cin gabashin kanta ta kasar Sin. Kasar Sin ta sha sanar da kungiyar EU da kasashe mambobinta da gaskiyar tashin hankalin da aka yi a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet, da kuma ci gaban da hukumomin jihar Tibet da abin ya shafa suka samu wajen gudanar da shari'a kan tashin hankalin. Rukunin Dalai shi ne ya shirya wannan tashin hankali, ya kuma zuga da a yi tashin hankalin, wadanda suke yunkurin neman 'yancin kan Tibet na gida da na kasashen waje suka yi cikin hadin guiwa. Lamarin ya sake nuna cewa, rukunin Dalai na neman kawo baraka ga kasar Sin, yana ta cutar mutane, wai ya nemi samun zaman lafiya kuma ba tare da nuna karfin tuwo ba, ban da wannan kuma, ya keta babban hakkin Bil'adama da kuma ka'idar 'yancin kai.(Tasallah)