Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-18 20:54:53    
Kura ta riga ta kwanta a birnin Lhasa na jihar Tibet

cri
Ran 18 ga wata, a nan Beijing, Qin Gang, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu kura ta kwanta a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, sa'an nan kuma, a galibi an maido da odar zaman al'ummar kasa a wurin.

A wannan rana, a gun taron manema labaru da ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta saba shiryawa, Qin ya yi nuni da cewa, hukumomin jihar Tibet da abin ya shafa suna nan suna gudanar da shari'a kan mummunan tashin hankali da aka samu a Lhasa a kwanan baya. Ya kara da cewa, kasar Sin ta sami isassun abubuwan shaida, kuma abubuwan gaskiya sun nuna cewa, rukunin Dalai shi ne ya shirya lamarin da aka samu a Lhasa, ya dade yana yunkurin yin wannan lamari, ya kuma zuga da a yi rikicin. Kasar Sin tana fatan kasashe da kungiyoyin duniya da abin ya shafa za su girmama abubuwan gaskiya, za su bambance abubuwan gaskiya, za su kuma tsaya tsayin daka kan adalci.

A kwanan baya, an haddasa mummunan tashin hankali a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet, wanda ya kawo wa mazaunan wurin babbar hasarar rayuka da dukiyoyi, haka kuma ya kawo babbar illa ga odar zaman al'ummar kasa a wurin.(Tasallah)