Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-18 19:02:19    
Firayin ministan kasar Sin ya gana da manema labaru na gida da na kasashen waje

cri

A ran 18 ga wata da safe an rufe cikakken zama na farko na majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin ta karo na 11 a nan birnin Beijing. Bayan wannan taro, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya gana da manema labarun gida da na kasashen waje, inda ya ba da amsoshi kan tunanin neman cigaban kasar Sin a cikin shekaru 5 masu zuwa da batutuwan da ke jawo hankulan mutane sosai yanzu a nan kasar Sin. Mr. Wen ya jaddada cewa, a cikin shekaru 5 masu zuwa, za a kara samun cigaban tattalin arziki da kyautatuwar zaman rayuwar jama'a da zaman al'ummar kasar. A waje daya kuma, aikin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da kasar Sin take yi zai kara samun cigaba.

Lokacin da yake zantawa kan ci gaban tattalin arziki, Wen Jiabao ya bayyana cewa, kayyade saurin hauhuwar farashin kayayyaki da raguwar darajar kudi nauyin farko ne da ke bisa wuyan gwamnatin kasar Sin. Ya ce, "Yawan hatsin da muka adana yanzu ya kai ton tsakanin miliyan 150 da dari 2. Kuma yawan muhimman kayayyakin masana'antu da ake samarwa ya kai fiye da ake bukata. Sabo da haka, idan mun aiwatar da manufofin da suka dace masu amfani, muna da imanin sarrafa halin hauhawar farashin kayayyaki cikin sauri da ake ciki."

Matsalar ta da manyan laifuffuka da ta auku a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta a kwanan nan ta zama batun da ke jawo hankulan mutane sosai. Wen Jiabao ya ce, muna da isassun abubuwan shaida da ke nuna cewa, wannan al'amari ne da rukunin Dalai Lama ya shirya. Mr. Wen ya ce, "Tun bayan da aka 'yantar da jihar Tibet cikin lumana da soma yin gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya zuwa yanzu, jihar Tibet ta samu cigaba da bunkasuwa sosai. an ce, wai gwamnatin kasar Sin ta gushe al'adun Tibet, karya ce kwata kwata. Ba ma kawai muna da karfin kiyaye kwanciyar hankali da odar zaman al'umma kamar yadda ya kamata a jihar Tibet ba, har ma za mu ci gaba da goyon bayan cigaban tattalin arziki da zaman al'ummar jihar, da kuma kyautata zaman rayuwar kabilu daban-daban da ke da zama a jihar da kiyaye al'adu da muhalli na Tibet. Ba za mu canja wannan matsayin da muke dauka ba gaba daya."

Sannan kuma, Mr. Wen ya bayyana cewa, idan Dalai Lama ya yi watsi da ra'ayinsa neman 'yanci kan Tibet, kuma ya amince da cewa, Tibet da Taiwan yankuna ne da ba za a iya kebe su daga kasar Sin ba. Gwamnatin kasar Sin za ta bude kofar yin shawarwari da shi a kowane lokaci.

Game da batun Taiwan, Wen Jiabao ya ce, dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta ki yarda da a shirya kada kuri'ar shigar da Taiwan cikin M.D.D. shi ne, idan irin wannan mataki ya samu nasara, tabbas ne za a canja halin Sin daya tak da ake ciki a tsakanin yankin Taiwan da babban yankin kasar Sin. Kuma tabbas ne za a kawo barazana ga dangantakar da ke tsakanin mashigin tekun Taiwan da ainihin moriyar jama'arsu da tsananta dangantakar da ke tsakaninsu da lalata halin zaman lafiya da ake ciki a tsakanin mashigin tekun Taiwan, har a yankunan Asiya da Pasifik. Sabo da haka, Mr. Wen ya ce, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin mashigin tekun Taiwan da neman cigabansu tare, ya kamata su zama muhimmin take ga dangantakar da ke tsakanin mashigin tekun Taiwan. Ya ce, "Ina son jaddada cewa, muna fatan za a iya komar da shawarwarin kawo zaman lafiya a tsakanin mashigin tekun Taiwan tun da wuri bisa ka'idar kasancewar Sin daya tak a duniya. Za mu iya tattaunawa kan kowane batun da ake son tattaunawa, ciki har da muhimmin batu na kawo karshen halin adawa da juna da ake ciki a tsakanin mashigin tekun Taiwan."

Yanzu wasu tsirarrun mutane suna kokarin mayar da gasar wasannin motsa jiki na Olympics da ya zama wani batun siyasa. Mr. Wen ya ce, shiya wata gasar wasannin motsa jiki ta Olympics a kasar Sin, gagarumin biki ne na jama'ar duk kasashen duniya. Wen ya ce, "Muna fatan za mu iya kara sada zumunta da hadin guiwa a tsakaninmu da jama'ar sauran kasashen duniya ta hanyar yin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics a nan kasar Sin. Muna fatan za mu iya shirya wannan gasa da kyau. 'Yan wasannin motsa jiki da jama'ar duk duniya za su ji dadin wannan gasa. Amma kasar Sin ba kasa ce mai arziki ba. Ba za mu iya magance wasu matsaloli ba lokacin da muke shirya wannan gasa. Amma jama'ar kasar Sin suna da sahihanci sosai wajen shirya wata gasar Olympics da kyau."