Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-18 16:52:26    
Wasu kasashen duniya sun ki yarda da sanya dalilin siyasa kan gasar wasannin Olympic ta Beijing bisa batun Tibet

cri
Ran 17 ga wata, dangane da lamarin mummunan tashin hankalin nan da wasu suka haddasa a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, wasu gwamnatoci da kafofin yada labaru na kasashen duniya sun yi nuni da cewa, ba su amince da sanya siyasa ba a kan gasar wasannin Olympic ta Beijing bisa batun Tibet.

A tasharta ta yanar gizo ta Internet, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Rasha ta ba da wata sanarwar cewa, jihar Tibet, wani bangare ne da ba a iya raba shi da kasar Sin ba. Rasha tana fatan kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba wajen hana afkuwar wannan mummunan aiki. Ba za ta amince da yunkurin yin amfani da siyasa ba a kan gasar wasanin Olympic ta lokacin zafi da za a yi a kasar Sin a shekarar da muke ciki.

Sa'an nan kuma, ministocin wasannin motsa jiki da shugabannin kwamitocin wasannin Olympic na kasashe 27 mambobin kungiyar tarayyar Turai wato EU sun bayyana cewa, ba za su amince da kauracewa gasar wasannin Olympic ta Beijing saboda lamarin da aka samu a jihar Tibet a kwanan baya.

Kazalika kuma, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Pakistan ya nuna cewa, Pakistan tana tsayawa tsayin daka kan kin yarda da dukkan yunkurin kawo illa ga mulkin kan kasar Sin da cikakken yankin kasar Sin. Yanzu a duk duniya babu wata kasa da ta amincewa da kasancewar wai kasar Tibet, wannan shi ne ra'ayi daya da dukkan kasashen duniya suka samu. Batun Tibet harkar gida ce ga kasar Sin. Pakistan ta ki yarda da yunkurin sanya dalilin siyasa kan gasar wasannin Olympic.(Tasallah)