Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-18 16:20:45    
Ayyukan kiyayeyanki mai dimbin duwatsu wato Shilin da kuma bayani kan bullowarsa

cri

A lokacin da suke yawo a yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin da ke lardin Yunnan na kasar Sin, mutane na kan yaba kuma suna mamakinsa, amma watakila su kan yi shakkar cewa, yaya wannan kyan karkara na hallita ya fito, a yaushe ne ya bullo, don me ya iya kasancewa har zuwa yanzu? A cikin shirinmu na yau, za mu amsa wadannan tambayoyi, za mu karanto muku labarin Shilin.

Game da bullowar Shilin, wata almara na bazuwa a tsakanin mazauna wurin. An ce, a can can can da, wani jarumin kabilar Sani mai suna Jinfenruoga ya nemi gina madatsar ruwa don kawo wa mutanen wurin alheri, shi ya sa ya yi dabara ya kori duwatsu daga kudu zuwa arewa, amma a gundumar Shilin, a yayin da gari ya kusan wayewa, kukan zakara ya bata kokarin da wannan jarumi ya yi, shi ya sa wadannan duwatsu suka tsaya a gundumar Shilin, ta haka an sami yanki mai dimbin duwatsu.

A gaskiya kuma, an yi shekaru kusan miliyan 300 ana fito da wannan yanki mai dimbin duwatsu Shilin, haka kuma bullowar Shilin na da sarkakiyya sosai. Shehun malami Liang Yongning, masani mai ilmin kayayyakin tarihi na duniya ya gaya mana cewa, 'Yau fiye da shekaru misalin miliyan 270 da suka wuce, wurin nan teku ne, daga baya, a sakamakon motsin tsalar duniya, an daga wannan wuri sannu a hankali, teku ya zama fili, fili mai lebur kuwa ya zama tudu. Duwatsun da aka samu a Shilin sun fito ne a cikin ruwa, sun kuma jure wuta bayan da duwatsu masu aman wuta suka barke. Motsin tsalar duniya ya ta daga wadannan duwatsu, a kwana a tashi aman wutar duwatsu sun bace, duwatsun sun sake bullowa. A zarihi kuma, ko wane dutse da aka samu a yanki mai dimbin duwatsu wato Shilin ya fito ne a zamani dabam dabam.'

A idanun kwararru masu ilmin sanin ma'adinai, daguwar tudun Yungui ta haifar da bullowar yankin mai dimbin duwatsu wato Shilin a Yunnan na kasar Sin, yankin Shilin ya nuna tarihin sauye-sauyen duniya ta fuskar tsarin yanayin kasa na Karst. Saboda irin muhimmiyar daraja a harkokin kimiyya da kuma kyan karkara na musamman da yankin Shilin na lardin Yunnan na kasar Sin ke nunawa, Hukumar ilmi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da shi a matsayin wurin yawon shakatawa na kasa da kasa domin kara wa mutane ilmin sanin ma'adinai a rukuni na farko a shekarar 2004. Sa'an nan kuma, a gun babban taron kayayyakin tarihi na duniya da ya kawo karshe a kwanan baya, bayan da aka dudduba da kada kuri'a, an tanadi yankin Shilin cikin takardar jerin kayayyakin tarihi na duniya. Masu yawon shakatawa na gida da na ketare da suka kawo wa yankin Shilin ziyara kan nuna babban yabo domin mamakinsa. Madam Sarry Archer, 'yar kasar Birtaniya, tana ziyara a wajen, ta ce, 'Yankin Shilin na da ban matukar mamaki a gare ni, ban taba gani ko kuma sanin irinsa a kasarmu Birtaniya ba tukuna.'

Saboda yankin Shilin na jawo hankali da amincewa daga kasashen duniya a kwana a tashi, miliyoyin masu yawon shakatawa kamar yadda madam Sarry Archer take suna kawo wa yankin Shilin ziyara.

Game da yadda za a bai wa masu yawon shakatawa kyakkyawar hidima da kuma kiyaye yankin Shilin yadda ya kamata, shugaba Li Zhengping na hukumar kula da shiyyar yawon shakatawa ta Shilin ya bayyana cewa, 'Hukumarmu ta soma tsara shirin raya shiyyar yawon shakatawa ta Shilin a shekarar 1985, ba a sami irin shiri da yawa a duk kasarmu ba. Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta zartas da kuma aiwatar da wannan shiri a shekarar 1987. Gundumar Shilin da gundumar Luliang ta kabilar Yi mai cin gashin kanta na lokacin can ta tsara 'ka'idojin kiyaye wuraren yawon shakatawa na gundumar Luliang' a shekarar 1991. Shirin da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta zartas da shi da kuma ka'idojin kiyayewa da hukumar wurin ta fito da su sun aza harsashi mai inganci a gare mu wajen kiyaye shiyyar Shilin.'

A shekarun baya da suka wuce, hukumar kula da shiyyar yawon shakatawa ta Shilin ta gayyaci kawarru da yawa a matsayin masu ba da shawara don raya shiyyar Shilin ta hanyar kimiyya.

Ban da wannan kuma, hukumar kiyaye muhalli na wurin kan sa ido da bincike kan yanayin iska da ruwa a shiyyar Shilin a lokaci-lokaci don tabbatar da ingancin iska a shiyyar. Dadin dadawa kuma, a kowace shekara, an shirya gagaruman harkokin yada ilmin kiyaye muhalli a kauyukan da ke dab da shiyyar Shilin don karfafa tunanin 'yan kauye na kiyaye albarkatun halittu.