Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-18 16:12:10    
Al'amarin ta da manyan laifuffuka masu tsanani rukunin Dalai Lama ne ya shirya sosai, in ji Wen Jiabao

cri

Firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya furta a ran 18 ga wata a nan birnin Beijing cewa, akwai isassun shaidun da suka tabbatar da cewa, kungiyar Dalai Lama ce ta shirya al'amarin barkewar mummunan tashin hankali a Lhasa.

An rufe cikakken zama na farko na taron majalisar jama'ar kasar Sin a karo na 11 a ran 18 ga wata a nan birnin Beijing. Yayin da Mr. Wen Jiabao yake ganawa da manema labarun kasar Sin da na kasashen waje bayan taron, ya ce, an samu barkewar mummunan tarzoma a kwanakin baya a jihar Tibet. Wannan ya lalata kwanciyar hankalin jihar Tibet, kuma ya haddasa asarar rayuka da dokiyoyin mutanen birnin Lhasa sosai. Kazalika, wannan al'amari ya karyata alkawarin da kungiyar Dalai Lama ta yi tun farko, wato ba za ta nemi 'yancin kan jihar ba, tana son yi mu'amala cikin ruwan sanyi.

Wen Jiabao ya furta cewa, ba ma kawai gwamnatin kasar Sin tana da karfin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin jihar Tibet da tabbatar da yanayin zaman al'umma yadda ya kamata ba, hatta ma za ta cigaba da nuna goyon baya ga bunkasuwar tattalin arziki da raya zaman al'umma a jihar Tibet don daga matsayin jin dadin zaman jama'ar kabilu daban daban na jihar da kuma kiyaye al'adu da muhallin halitta na jihar.(Lami)