Wakilin gidan rediyon CRI ya ruwaito mana labari cewar, Wen Jiabao, wanda ya sake lashe zaben firaministan kasar Sin nan ba da jimawa ba ya bayyana yau 18 ga wata a nan Beijing cewar, batutuwa hudu da gwamnatin Sin za ta maida hankalinta sosai a kai su ne: Na farko, bunkasa tattalin arziki cikin sauri ba tare da tangarda ba. Na biyu shi ne, yunkurin samun sabbin nasarori wajen yiwa tsarin tattalin arziki da na siyasa kwaskwarima. Na uku wato sa kaimi ga shimfida turbar adalci a zamantakewar al'umma. Na hudu wato na karshe shi ne, inganta ayyukan raya kyawawan al'adu irin na gurguzu.
An rufe cikakken zama na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11 yau 18 ga wata a nan birnin Beijing. Yayin da firaminista Wen ke ganawa da manema labaru na gida da na waje bayan taron, ya yi nuni da cewar, a halin yanzu, da farko, yayin da take raya tattalin arziki, ya kamata kasar Sin ta sanya matukar kokari wajen warware matsalolin rashin kwanciyar hankali, da rashin adalci, da cigaba marar dorewa, musamman ma matsalar tsawwalar farashin kaya fiye da kima, ta yadda za a samu habakar tattalin arziki da kyau kuma cikin sauri. Na biyu shi ne, ya kamata mu sabunta tunaninmu, da sa kaimi ga ayyukan yin gyare-gyare da kirkire-kirkire, domin cimma tudun-dafawa a fannin yiwa tsarin tattalin arziki da na harkokin siyasa gyare-gyare. Na uku shi ne, daukaka cigaban zaman adalci a duk zamantakewar al'umma, da mutuntawa da kuma kiyaye halaltaccen hakkin dan Adam, da samar da zarafi daidai-wa-daida ga kowane dan Adam a karkashin ikon 'yancin kai da adalci. Na hudu wato na karshe shi ne, kamata ya yi a inganta ayyukan raya al'adu a zaman rayuwar jama'a, ta yadda kasar Sin za ta kasance wata kasa cike da nagartattun al'adu.(Murtala)
|