Wakilin gidan rediyon CRI ya ruwaito mana labari cewar, shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo ya bayyana yau 18 ga wata a nan Beijing cewar, kamata ya yi a yi kokari wajen cimma da kuma kare babbar moriyar al'ummar kasar da kyau.
Wu Bangguo ya fadi haka ne a wajen bikin rufe taron shekara-shekara na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a yau. Ya ce, yayin da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11, da zaunannen kwamitinta suke nacewa ga bin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya kamata su hada "jama'ar kasar Sin su ne suke mulkin Sin" da "gudanar da harkokin mulkin kasa bisa dokar shari'a" yadda ya kamata, da nacewa ga bin tsarin majalisar wakilan jama'a da kyau, da kuma kyautata shi, da tabbatar da manyan tsare-tsare na gudanar da harkokin mulkin kasa bisa doka, da aiwatar da su yadda ya kamata.
Mr. Wu ya kuma kara da cewar, dole ne a tsaya tsayin daka kan kafa dokokin shari'a ta hanyar dimokuradiyya kuma daidai bisa kimiyya, da daga matsayin kafa dokokin shari'a, ta yadda dokokin shari'a za su kara taka rawarsu wajen bada jagoranci da tabbaci ga zaman siyasa da zaman rayuwar jama'a na kasar Sin. A waje daya kuma, Mr. Wu ya ce, kamata ya yi a cigaba da inganta da kyautata harkokin sa ido, ta yadda majalisar wakilan jama'ar kasar Sin za ta kara taka rawa ta sa ido wajen daukaka cigaban gudanar da harkokin gwamnati bisa doka, da aiwatar da dokokin shari'a cikin halin daidaici, tare kuma da kiyaye babbar moriyar al'umma.(Murtala)
|