Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-17 21:08:36    
An riga an tabbatar da kwanciyar hankali a birnin Lhasa

cri

A ran 17 ga wata, Mr. Qiangba Puncog, shugaban jihar Tibet mai cin gashin kanta kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing, cewar ya zuwa yanzu an riga an tabbatar da kwanciyar hankali da odar zaman lafiya a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta.

Mr. Qiangba Pincog ya fadi haka ne a gun wani taron manema labaru da ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a wannan rana.

Mr. Qiangba Pincog ya bayyana cewa, al'amarin ta da manyan laifuffuka masu tsanani da aka yi a cikin birnin Lhasa a ran 14 ga wata, rukunin Dalai Lama ne ya shirya sosai, kuma wadanda suke yunkurin neman 'yancin kan Tibet na gida da na kasashen waje suka yi cikin hadin guiwa. Sabo da haka, jama'ar kabilu daban-daban na Tibet sun nuna matukar bacin rai, kuma sun yi Allah wadai da wannan al'amari. Jihar Tibet mai cin gashin kanta ta riga ta dauki matakan yaki da wannan laifin nuna karfin tuwo da aka yi. Ya jaddada cewa, ko shakka babu ba za a iya canja niyyar adawa da yunkurin ballewa daga kasar Sin ba da tabbatar da dinkuwar kasar Sin bai daya da tabbatar da kwanciyar hankalin zaman al'umma na jama'ar kabilu daban-daban na Tibet ba. Tabbas ne dukkan yunkurin lalata halin kwanciyar hankali da ake ciki a Tibet da kawo wa kasar Sin baraka yunkuri ne mai bakin jini, kuma tabbas ne zai ci tura.

A ran 14 ga wata, an samu al'amarin ta da manyan laifuffuka masu tsanani sosai a cikin birnin Lhasa. Bisa labarin da aka samu yanzu, yawan gidaje da kantunan da masu laifuffuka suka kona ya kai fiye da 210, yawan motocin da aka kona ya kai fiye da 50. A waje daya kuma, mutane fararren hula da suka mutu sakamakon aka kona su, ko aka yanka su da wuka ya kai 13. Wannan al'amari ya yi hasara sosai ga rayuka da dukiyoyin jama'ar wurin, kuma an lalata odar zaman al'ummar wurin ainun. (Sanusi Chen)