Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-17 16:25:14    
Sharadin gidajen kwana na iyalai masu fama da talauci da yawansu ya kai dubu 950 ya kyautatu a kasar Sin

cri

Wakilin gidan rediyon CRI ya ruwaito mana labari cewar, yayin da mataimakin ministan harkokin gidajen kwana da raya birane da kauyuka na kasar Sin Qi Ji ke zantawa da manema labaru na gida da na waje yau 17 ga wata a nan birnin Beijing, ya bayyana cewar, a karkashin tsarin yin hayar gidajen kwana cikin farashin mai rahusa, sharadin gidajen kwana na iyalai masu fama da talauci da adadinsu ya kai dubu 950 ya sami kyautatuwa a kasar Sin.

Mr. Qi ya ce, tsarin yin hayar gidajen kwana cikin farashi mai rahusa wani kashi ne mafi muhimmanci na tsarin bada tabbaci ga gidajen kwana wanda ake gudanarwa a halin yanzu a nan kasar Sin. Tun daga farkon shekarar da ta shude, an fara gaggauta raya tsarin yin hayar gidajen kwana cikin farashi mai rahusa, kuma yawan iyalai masu fama da talauci wadanda suka ci gajiyar tsarin ya kara karuwa.

Mr. Qi ya kara da cewar, kason da gwamnatin kasar Sin ta ware ma raya tsarin yin hayar gidajen kwana cikin farashi mai rahusa zai kai kudin Sin Yuan biliyan 6.8, wato ya karu da biliyan 1.7 idan an kwatanta shi da na shekarar bara. A waje daya kuma, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta bukaci wurare daban-daban na kasar da su kara kebe kudi ga aikin raya tsarin yin hayar gidajen kwana cikin farashi mai rahusa.(Murtala)