Matakan ba da taimako da ma'aikatar kimiyya da fasaha na kasar Sin da hukumomin nazari da abin ya shafa suka samar wa Tibet sun ba da tabbaci ga bunkasuwar kimiyya da fasaha a jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta.
A cikin shekarun nan, ma'aikatar kimiyya da fasaha da hukumomin nazari sun kara karfinsu wajen nuna goyon baya ga harkokin kimiyya da fasaha na jihar Tibet. Yanzu, jihar Tibet tana da wadansu ayyuka da suka zama manyan ayyukan kimiyya da fasaha na kasar Sin, kuma ta samu kudin taimako da yawansa ya kai kusan kudin Sin Yuan miliyan 80, wannan ya ba da tabbaci ga ayyukan kimiyya da fasaha na jihar Tibet a fannin kudi.
Ban da wannan kuma, hadin gwiwa dake tsakanin jihar Tibet da cibiyar nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin yana ta kara karuwa, tun daga shekarar badi, cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta kasar Sin za ta zuba jari da yawansa ya kai kudin Sin Yuan miliyan 6 a kowace shekara, don sa kaimi ga bunkasuwar kimiyya da fasaha na jihar Tibet. (Zubairu)
|