Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-17 16:06:07    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Jihar Tibet ta kasar Sin za ta fara aikin zaben "shahararrun likitoci masu aikin likitancin gargajiya na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta" a karo na farko, yanzu ana nan ana gabatar da rahoton rajista domin shiga zaben.

Kwanan baya, mun sami labari daga sashen kula da likitanci da magungunan gargajiya na hukumar kiwon lafiya ta jihar Tibet cewa, shahararrun likitoci masu aikin likitancin gargajiya na Tibet suna nufin kwararrun mutane masu fasahar likitancin gargajiya na Tobet, wadanda suke aiki a gurabun likitanci, kuma sun yi fifitattun ayyuka kan ilmin likitanci, wadanda kuma ke yin kokarin kirkira wajen kimiyya da fasaha don sa kaimi ga bunkasa aikin likitanci, kuma sun samu nasarori a bayyane a fannin rigakafi da warka da manyan cututtuka, sabo da haka sun yi suna sosai daga zaman al'umma kuma sun sami amincewa daga wajen abokan aikinsu.

Likitanci da magungunan gargajiya na Tibet wani muhimmin kashi ne daga cikin likitanci da magungunan gargajiya na kasar Sin, yau da shekaru fiye da 2000 da aka samu ci gaba wajen bunkasa likitanci da magungunan gargajiya na Tibet, sun ba da babban taimako ga lafiyar jama'ar jihar Tibet ta kasar Sin.

---- Mun sami labari daga wajen taron shugabannin hukumomin al'adun jihar Tibet da aka yi kwanan baya cewa, yanzu yawan wuraren nishadi da ake da su a jihar ya karu daga 910 na shekarar 2002 zuwa 2596, yawan ma'aikatan da suke aiki a wadannan wurare su ma sun karu daga dubban mutane na shekarar 2002 zuwa 18,350 na yanzu, kasuwannin al'adu suna cike da arziki da wadata., nau'o'in kayayyakin da aka sayar da yawan harajin da aka buga daga wajen al'adu suna ta karuwa a kowace shekara.

Mr. Nimaciren, shugaban hukumar al'adu ta jihar tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, an ware makudan kudade domin gudanar da harkokin al'adu, ta haka ne tsarin al'adu da aka kafa a jihar ya samu kyautatuwa sannu a hankali, matsayin tafiyar da harkokin al'adu kuma ya yi ta samun ingantuwa, an riga an zuba kudi daga fannoni daban-daban, kuma an samu ci gaba ta hanyoyi da yawa, ana nan ana samun bunkasuwa ta hanyar kara wa juna himma.

An bayyana cewa, yanzu jihar Tibet tana da kamfanonin yawon shakatawa na al'adu, da kamfanonin kawata gidaje domin yin talla, da dakunan zane-zanen fasaha, da gidajen shan ti, da wuraren hutu daban-daban wadanda yawansu ya kai fiye da 3,000, an kusan bude kasuwar nuna wasanni, kuma an samu ci gaba da sauri wajen bude wuraren yawon shakatawa cikin gidajen 'yan kabilar Tibet, kuma ana ta kara samun kwarin gwiwa wajen samar da kayayyaki ga kasuwannin al'adu.