Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-17 15:38:14    
Kasashen Sudan da Chadi sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya

cri

A ranar 13 ga wata da dare, shugaba Omar al-Bashir na kasar Sudan, da takwaransa na kasar Chadi Idriss deby itno, sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal, ta yadda aka kara kafa tushen zaman lafiya wajen warware rikicin bakin iyakar kasashen biyu, da kara nuna amincewa ga juna, da kuma kyautata dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Kasashen Sudan da Chadi su cimma yarjejeniyar zaman lafiya ne a lokacin taron koli na kasashen musulmi a zama na 11 da aka shirya a birnin Dakar. Babban sakataren M.D.D. Ban Ki-Moon, da kuma shugaban kasar Senegal Abdoulaye wade, da dai sauransu, su ma sun halarci bikin sa hannu kan yarjejeniyar. Yarjejeniyar ta kayyade cewa, kasashen biyu su dauki alkawarin hana dukkan ayyukan dakarun da ke adawa da gwamanti, da hana yin amfani da yankunan kasashen biyu, domin kawo lahani ga zaman lafiyar kasashen biyu. Kazalika kuma, kasashen Kongo Brazaville, da Libya, da Senegal, da Ghabon, da Eriteria, da dai sauransu, da kuma AU, wato kungiyar tarrayar kasashen Afrika, za su kafa rundunar sojojin tsaro, don ba da tabbaci da sa ido kan zaman lafiyar bakin iyakar kasashen biyu. Bayan haka kuma, bagarorin biyu sun amince da wadannan kasashe da su kafa kungiyar ma'amala, don sa ido kan halin kiyaye zaman lafiyar da ake ciki a tsakanin kasashen Chadi da Sudan.



Kasashen Sudan da Chadi sun taba sada zumunta cikin dogon lokaci. Rikicin da ke tsakanin gwamnatocin kasashen biyu, da kuma tsakanin dakarun da ke adawa da gwamnati na kasashen biyu na kansu, shi ne muhimmin dalilin da ke lalata dangantaka a tsakanin kasashen biyu. A waje daya kuma, bayan bullowar matsalar shiyyar Darfur, bisa zugar kasashen yamma, dakarun da ke adawa da gwamnati na shiyyar Darfur ta kasar Sudan, su kan kutsa a yankin da ke gabashin kasar Chadi, don tattara dakaru. A sakamakon haka, halin da ake ciki a bakin iyakar kasashen biyu yana ta kara tsanani a kwana a tashi, har ma sun taba katse dangantakar diplomasiya a tsakaninsu. A daidai ranar bude taron koli na kasashen musulmi na wannan karo, kasar Chadi ta zargi gwamnatin kasar Sudan da ta nuna goyon baya ga dakarun da ke adawa da gwamnati na kasar Chadi don shiga kasar, kuma ta bayyana cewa kasar Sudan ta aika da rundunar sojoji zuwa yankin da ke gabashin kasar Chadi. Amma, kasar Sudan ta musunta haka.



Kafin kiran taron koli na kasashen musulmi a zama na 11, shugaba Wade na kasar Senegal ya sanar da cewa, zai gayyaci shugaba Al-Bashir na kasar Sudan, da kuma shugaba Deby Itno na kasar Chadi da su yi shawarwari kai tsaye a lokacin taron, don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a bakin iyakar kasashen biyu. A waje daya kuma, Mr. Wade ya gayyaci babban sakataren M.D.D. Ban Ki-Moon, da kuma shugabanni na wasu kasashen Afrika da su halarci shawarwari a tsakanin shugabannin kasashen Chadi da Sudan. Ya bayyana cewa, yana fatan shawarwarin za su ba da taimako mai yakini don tabbatar da zaman karko a shiyyar. Mr. Al-Bashir ya bayyana kafin shawarwarin cewa, kasashen Sudan da Chadi sun taba cimma yarjejeniyoyin zaman lafiya har sau biyar, amma ba a gudanar da su kamar yadda yakamata ba. Saboda haka, ya yi shakka ga ko wajibi ne a kara cimma sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya ko a'a, da kuma ko za a iya gudanar da sabuwar yarjejeniya kamar yadda ya kamata ko a'a. Amma, kasar Chadi ta bayyana cewa, tana fatan cimma yarjejeniya tare da kasar Sudan kan warware rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu, kuma za ta cika alkawaran da za ta yi a birnin Dakar. A cikin yarjejeniyar zaman lafiya da kasashen Sudan da Chadi suka cimma a ranar 13 ga wata, kasashen biyu sun jaddada cewa, za su bi yarjejeniyoyi guda biyar da suka cimma a da.

Manazarta suna ganin cewa, kasashen Sudan da Chadi su ne kasashen da ke bukatar samun bunkasuwa cikin gaggawa a babban yankin Afrika, kiyaye zaman lafiyarsu kuma, zai kafa hali mai dacewa ga bunkasuwarsu. Gudanar da yarjejeniyar zaman lafiya ta kasashen biyu, za ta zama sabon masomi na kyakkyawar dangantakar makwabtaka da ke tsakaninsu.