Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-17 15:31:59    
Kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan ba da tabbaci ga ingancin abinci da magunguna na wasanin Olympic

cri

Wani jami'in hukumar sa ido da kula da ingancin abinci da maganganu ta kasar Sin ya furta a ran 16 ga wata a nan birnin Benjing cewa, Kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan ba da tabbaci ga ingancin abinci da magunguna na wasanin Olympic.

Shugaban sashen ingancin abinci na hukumar sa ido da kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Sin Sun Xianze ya furta a yayin da yake ganawa da manema labarun kasar da kasashen waje cewa, kasar Sin ta samar da abincin wasannin Olympic na Beijing bisa ma'aunin koli na duniya; ta sa ido kan kamfannoni masu samar da abinci da kayayyaki ga wasannin Olympic da kamfanonin ketare da kwamitin wasannin Olympic ya ba su iznin samar da kayayyaki ga wasannin Olympic a fannin muhallinsu da ingancinsu da yawan sinadarin hormone dake kasancewa a cikin kayayyakinsu, a sa'i daya kuma, ta kafa tsarin sa ido kan ingancin abincin wasannin Olympic, ta yadda za a karfafa tsarin ko ta kwana don daidaita batutuwan da za su faruwa cikin gaggawa, da tattarawa da watsa labarai, da kuma aikin sa ido na yau da kullum.(Lami)